Kasar Saudiyya tace ta gama da yaduwar farfagandar kasar Iran a nahiyar Afirka
- Mun karya karfin Iran a Afirka inji Yarima mai jiran gadon Saudiyya
- Muhammad Bin Salman yace kasarsa tayi nasarar karya tasirin Iran da kawayenta a Afirka wanda ya jaw cece kuce
- Ba'a ga-maciji tsakani larabawa da Iraniyawa
A wata hirar da jaridar Times ta Amurka tayi da Yariman yace kasar sa tayi aiki tukuru a Afirka don ganin ta rage tasirin Iran a Nahiyar,a inda tayi nasarar karya karfin kasar Iran a Afirka da kaso 95 cikin 100.
Jami'i a cibiyar tsara dabarun mulki da tunkarar matsaloli na kasar Saudiyya, Dr Zayeed Al-Amri ya yi karin haske kan manufar Yariman inda yake cewa
"Abinda Yarima yake nufi tun bayan da ya bayyana shirinsa na tunkarar makiya, Saudiyya tayi nasarar karya tanadin Iran a Yemen, Somaliya, Djibouti da Sudan yadda ta lalata yunkurin ta na kafa makamanciyar kungiyar Hizbullah a Najeriya da hana Ibrahim Zakzaky yin juyin mulki a kasar."
Toh saidai duk da haka wasu na ganin kasar ta Saudiyya tanayin azarbabi da cusa kanta fiye da misali kan ikirarin da take na karya karfin kasar ta Iran a Afirka.
Inda a daidai lokacin Yariman mai jiran gado yake tsuke bakin aljihu yake rage kudaden hannayen jari a Afirka yake kuma yaki kan yada akidar Wahabiyanci.
DUBA WANNAN: Rigimar Larai da Turai: Janar daga Iran ya mayar wa da Saudiyya martani
Sai dai a hannu guda kuma kasar ta Iran na kara himma don ganin ta kulla sababbin huldodi da Afirka da bada guraben karatun ilimin kimiyya da fasaha ga daliban na Afirka.
Yanzu haka ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zareef ya isa kasar Senegal a rangadin da yake a kasashen Afirka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng