'Yan Shi'a sun yi zanga-zanga da gawar mabiyin su da jami'an 'Yan Sanda suka harbe a garin Abuja

'Yan Shi'a sun yi zanga-zanga da gawar mabiyin su da jami'an 'Yan Sanda suka harbe a garin Abuja

A cikin wani Bidiyo da shafin jaridar Sahara Reporters suka yada ya bayyana yadda mambobin kungiyar IMN (Islamic Movement in Nigeria) watau kungiyar Shi'a suka gudanar da zanga-zanga da gawar wani mabiyin su da jami'an 'Yan sanda suka batar a yayin wata zanga-zanga a garin Abuja.

Kungiyar ta gudanar da zanga-zanga ne a gaban Shelkwatar cibiyar kare hakkin dan Adam ta Najeriya dake babban birnin tarayya na Abuja a sakamakon nuna rashin amincewa na tsare shugabanta Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da gwamnati ke ci gaba da yi.

Kalli Bidiyon zanga-zangar

Sai gashi cikin wannan bidiyo da shafin na Sahara Reporters ya yada ya bayyana yadda 'yan Shi'ar suka gudanar da zanga-zanga dauke da gawar wani mabiyin su, Ahmad Rufai Dodo, da rayuwar sa ta salwanta a hannun jami'an tsaro na 'yan sanda sakamakon karen batta da ya afku.

KARANTA KUMA: Yadda Kwayoyin halittu ke habaka da sanadin Barasa wajen dakile wasu cututtuka a jikin dan Adam

Kungiyar dai ta bayyana cewa, Ahmad Dodo ya rasa rayuwar sa ne a yayin da yake yunkurin arcewa daga farfajiyar zanga-zanga bayan da jami'an 'yan sanda suka tirnike su da barkonon tsohuwa sa'annan suka fara harba harsashai kan mai uwa da wabi.

Legit.ng da sanadin rahotannin ta fahimci cewa, jami'an na 'yan sanda sun harbi Dodo a goshin sa inda yace ga garin ku nan bayan an garzaya da shi asibiti, yayin da wannan karen batta ya raunata kimanin 'yan kungiyar hudu kamar yadda ta bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng