Matasa sun fusata, sun hallaka dan sanda

Matasa sun fusata, sun hallaka dan sanda

Wani rikici ya barke a Amandugba, karamar hukumar Isu na jihar Imo ranan Lahadi yayinda wasu mafusatan matasa suka kashe wani jami’in dan sanda mai suna, Chijioke Okorie, kan laifin kisan wani bako mai suna, Ojiegbr Azuoku.

Game da cewan wani idon shaida wand aka sakaye sunansa, rikici ya barke ne a cikin gidan masaukar baki misalin karfe 8:45 na dare inda jami’an tsaro suka hallara.

Yayinda yan sanda suka isa wajen, Sajen Okorie ya harba harsashi cikin jama’a wanda ya sabbaba mutuwan daya daga cikin mutanen da ke wajen.

Matasa sun fusata, sun hallaka dan sanda
Matasa sun fusata, sun hallaka dan sanda

Da wuri mutanen da ke wajen suka far wa jami’in dan sandan suka kashe shi har lahira.

Yace: “Wannan abun takaicin ya faru ne daren Lahadi. Ana rikici a wani Otel mai suna Golden C. Sai yan sanda suka zo. Shigowansu ke da wuya, sai daga cikinsu ya harba bindiga ba gaira ba dalili kuma ya kashe mutum daya; kafin a isa asibiti, ya mutu.”

“Mutanen da wajen kuma suka suburbudi wannan dan sanda har lahira. A yanzu haka, akwai tashin hankali a unguwan.”

KU KARANTA: Amincewar masu fada aji na jam’iyyar APC cewa Oshiomole ya gajeshi yarinta ne - Oyegun

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Andrew Enwerem, ya tabbatar da wannan labara inda yace kwanishanan yan sandan ya bada umurnin bincike cikin al’amarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng