Allah yayiwa babbar Yayar Sule Lamido rasuwa
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa Allah yayiwa babbar yayar btsohon gwamnan jihar Jigawa kuma dan takarar shugaban kasa a yanzu, Sule lamiso rasuwa.
Marigayiyar Hajiya Yahanasu Lamido ta rasu ne a safiya yau Laraba, 25 ga watan Afrilu.
Muna rokon Allah ya jikanta da rahama, ya sa aljanna ta zama makoma a gareta da sauran al'ummar musulmi.
A kwanakin baya Legit.ng ta rahoto labarin mutuwar wasu yan majalisa uku masu wakiltan jihar Kogi, Katsina da kuma jihar Bauchi.
KU KARANTA KUMA: Anyi gaggarumin zanga-zanga a garin Makurdi sakamakon kisan manyan limamai da mabiyansu 17 da makiyaya sukayi (hotuna)
Rasuwan nasu ya biyo juna ne inda hakan ya daga ran mutane da dama musamman yan majalisar, harma kakakin majalisa, Yakubu Dogara ya bayyana damuwar karara akan yawan mace-macen nasu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng