Matan Najeriya: Albashi da ya dace ace suna samu - ra'ayin wani marubuci

Matan Najeriya: Albashi da ya dace ace suna samu - ra'ayin wani marubuci

- Basa biyanmu da kudi! Maza kawai suke biya. Suna biyanmu ne da tsakin shinkafa." wannan kalaman wata mata ne dake aiki a kamfanin sarrafa shinkafa

- Wannan kalaman na nuna yanda har a gurin albashi ake nuna bambancin jinsi a Najeriya

- Matan da ke aiki a kamfanin sarrafa shinkafar ana bambanta su da mazan ko ta gurin albashi. Ba wai don basu da himma ba, kawai dai saboda bambancin jinsi wanda al'ada ce kawai tazo dashi

Matan Najeriya: Albashi da ya dace ace suna samu - ra'ayin wani marubuci
Matan Najeriya: Albashi da ya dace ace suna samu - ra'ayin wani marubuci

Matan bazasu more ma guminsu ba saboda su "Mata" ne wadanda al'ada bata daidaita su ko ta gurin kudi ne da 'yan uwan halittarsu. Hakan yana nufin ba kwazonka ne yake sa ka samu kudi ba.

Ba abin mamaki bane a rahoton, 2017 na Global Gender Gap wanda World Economic Forum (WEF) ta saki kwanan nan yace Najeriya ce kasa ta 122 a cikin 144 a rufe gibin jinsi.

Rahoton WEF din yana duba matsayin jinsi ne a wasu kasashen ta fuskar tattalin arziki, ilimi, lafiya da dogaro da kuma cigaba ta fuskar siyasa. Ana duban ne don rage kalubalen da ake fuskanta na gibin jinsi da kuma damar rage ta.

Tunda kungiyar ta fara duba wannan matsalar shekaru 10 da suka wuce, kungiyar ta bayyana cewa da farko dai abubuwan babu cigaba.

A rahoton da ta saki na 2 ga watan Nuwamba, 2017. Tace "kashi 68 cikin dari na gibin jinsi ya rufe yanzu, ana samun raguwar bambancin jinsi a guraren aiki da kuma wakilcin siyasa."

DUBA WANNAN: Yawan yaran da aka ceto daga almajirta a jihar Kano ya zuwa yanzu

Tunda kungiyar ta fara duba wannan matsalar shekaru 10 da suka wuce, kungiyar ta bayyana cewa da farko dai abubuwan babu cigaba.

A rahoton da ta saki na 2 ga watan Nuwamba, 2017. Tace "kashi 68 cikin dari na gibin jinsi ya rufe yanzu, ana samun raguwar bambancin jinsi a guraren aiki da kuma wakilcin siyasa."

Masu kare hakkin jinsi da yawa suna kuka da halin da ake ciki a Najeriya. Tsohuwar ministan ilimi Oby Ezekwesili tace gaskiya halin da kasar ke ciki babu kyau, Dole ne mu gyara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng