Alkalin Alkalan Najeriya ya jadadda goyon bayansa ga Buhari game da yaki da rashawa

Alkalin Alkalan Najeriya ya jadadda goyon bayansa ga Buhari game da yaki da rashawa

Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen ya bayyana cewa sashin shari’a na goyon bayan kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari game game da yaki da rashawa, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Walter ya bayyana haka ne a hirar da yayi da manema labaru bayan fitowarsa daga wata ganawar sirri da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige manyan Fastoci 2, masu bauta guda 15 a Cocin jihar Benuwe

Walter ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne ga shugaba Buhari don bayyana ma Buhari irin kokarin da suke yi a yaki da da cin hanci da rashawa, da kuma abubuwan da suke faruwa a sashin shari’ar kasar nan.

Alkalin Alkalan Najeriya ya jadadda goyon bayansa ga Buhari game da yaki da rashawa
Alkalin Alkalan Najeriya da Buhari

Alkalin Alkalai ya musanta zarge zargen da ake musu na cewa wai Alkalai na jan kafa a shari’un da suke yi, musamman wadanda suka shafi cin hanci da rashawa, inda ya kara da cewa fannin shari’a na iya bakin kokarinta wajen gaggauta kammala shari’un.

“Babu yadda za’a yi ace haka nan Alkali ya guji zaman Kotu ba tare da wani dalili ba, ko kuma ace alkali ya kammala sauraron kararrakin dake gabansu, amma kuma yaki yanke hukunci, don haka har in dai Alkali zai saurari kararraki, sa’annan kuma saboda wasu dalilai ya dage sauraron karar, bai kamata a zarge shi da jan kafa ba.” Inji shi.

Daga karshe yace a yanzu haka sashin shari’a na jiran sashin zartarwa ta kafa Kotuna na musamman da gurfanar da barayin gwamnati, su kuma zasu tura Alkalai don gudanar da ayyukansu a wadannan Kotunan, haka zalika suna taka muhimmin rawa wajen rage yawan mazauna gidan Yari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng