Kudin ruwa da ajiyar marigayi Abacha ta tara a Switzerland ya kai miliyoyi
- Abacha ya 'adana kudadden Najeriya biliyoyi da sunansa a kasashen waje
- Kudin ya shekara 20 suna juyawa, har ya haifar da ribar biliyoyi
- Kudaden na dawowa Najeriya a hankali, kudin na talakawa ne
Kasar Switzerland ta ce ta dawo wa da Najeriya duka kudin da tsohon shugaban kasar mulkin soja General Sani Abacha ya kai ajiya harda ribar Dala Miliyan Daya da rabi.
Ambassadan kasar Switzerland na Najeriya Pio Wennubst, sannan kuma shugaban (Global Cooperation Department, Swiss Agency for Development and Cooperation), ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya hakan a birnin New York.
Wennbust yace kasar Switzerland ta dawo wa da gwamnatin tarayya kimanin dala miliyan 322.5, wanda yayi dai dai da naira biliyan 116.11. A cewar sa, kudin na gaskiya sune dala miliyan 321.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta bayyana cewar ta karbi ricit na dala miliyan 322.51 daga kasar Switzerland, wanda yake daga cikin kudin da gwamnatin Sani Abacha ta boye a kasar. Sanarwar ta fito daga bakin Oluyinka Akintunde, babban mai bawa Ministar Kudi, Kemi Adeosun shawara, inda ya tabbatar da cewar gwamnati ta karbi kudin daga kasar ta Switzerland.
Akintunde yace; "Mun bayyana cewar a ranar 18 ga watan Disamba dinann ne babban bankin Najeriya (CBN) ya karbi kudi kimanin dala 322,515,931.83, wanda yayi dai dai da kimanin naira 116,105,735,458.80, daga wurin gwamnatin kasar Switzerland".
Bayan haka Wennubst ya kara tabbatar da shigowar kudin inda yace; "Mun dawo da dala miliyan 321 tare da ribar dala miliyan 1.5 inda ya kama dala miliyan 322.5.
DUBA WANNAN: Farfesa mai fesarwa ya shiga hannu
Har ila yau wakilin kasar ta Switzerland yace, an mayar da kudaden ga gwamnatin Najeriyan ba tare da bata wani lokaci ba."
A cewar sa, kudaden na daga cikin gudunmawar da gwamnatin Najeriya ta wancan lokacin ta bayar a matsayin kudin kyautata shirin tsarin zamantakewar kasashen.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng