Fusattun matasa sun halaka wani saja da ya kashe wani bako a otal

Fusattun matasa sun halaka wani saja da ya kashe wani bako a otal

Wani abin bakin ciki ya afku a garin Amangduba a karamar hukumar Isu da ke jihar Imo a ranar Lahadi bayan fusatatun mutane sun kashe Saja Chijioke Okarie saboda ya kashe wani bako mai suna Ojiegbe Azuoko a wani Otal.

Jaridar Daily ta bayyana cewa hatsarin ya afkune a Golden C wani sabon otal da aka bude. Hukumar yan sanda ta Isu ta bayar umarnin rufe otal din bayan wanda aka yanka ya bayar da rahoto kafin mutuwarsa.

Fusattun matasa sun halaka wani saja da ya kashe wani bako a otal
Fusattun matasa sun halaka wani saja da ya kashe wani bako a otal

Mai bayar labarin wanda ya nemi a sakaya sunan sa yace sunji ana fada a cikin otal din da misalin 8:45 na dare.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe wani gawurtacen 'dan ta'ada a jihar Akwa Ibom

Hakan shiya janyo hankulan mutane da kuma yan sandan dake kan aiki zuwa wajen. A cikin hotel din sergeant Okarie yace an koreshi a cikin mutane wanda hakan ya janyo daya daga cikin mazauna otal din ya rasa ransa.

Mutanen wajen suna zargin sergeant Okarie inda sukayi kokarin kashe shi.

Mai maganar yace an sumu wata yar hatsaniya a sabon otal din da aka bude na Golden C wanda hakan yaja hankulan mutane da kuma jami'an yan sanda zuwa wajen.

Inda a take daya daga cikin yan sandan ya bude wuta ba tare da wani bincike ba inda yayi sanadiyyar mutuwar mutum daya. Su kuma mutane suka rufarwa wannan dan sanda inda wata sabuwar hatsaniya ta runcabe tsakanin mazauna wajen da yan sanda.

Domin tabbatar da afkuwar lamarin Shugaba Andrew Enwerem yace kwamishinan yan sanda ya bada umarni da ayi bincike akan lamarin. Kwamishinan ya bada umarnin gaggawa akan binciken. Inda hatsaniyar ta lafa mutane suka bawa yan sanda damar aiwatar da aikinsu.

A dauke gawar dan sandan data bakon zuwa wajen aje gawawaki a asibiti.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel