Matasa Kadara ce mai Muhimmiyar Daraja ga kowace Kasa - Jakadan UN

Matasa Kadara ce mai Muhimmiyar Daraja ga kowace Kasa - Jakadan UN

Jakadiyar Babban Sakataren majalisar dinkin duniya akan Matasa, Ms Jayathma Wickramanayake ta bayyana cewa, matasa wata muhimmiyar kadara ce mai matukar muhimmanci ga kowace kasa a madadin zama matsala a gare ta.

Jakadiyar ta yi wannan Fashin Baki ne a yayin gabatar da sakamakon wani bincike mai zaman kansa da aka gudanar akan Matasa, Zaman Lafiya da kuma Tsaro.

Jayathma ta bayyana cewa sakamakon binciken ya tabbatar da wasu muhimman ababe biyu da suke buƙatar lura ta gaggawa.

Jayathma Wickramanayake
Jayathma Wickramanayake

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, muhimmin abu na farko kamar yadda Jayathma ta bayyana shine yadda ake ci gaba da rashin yarda da kuma rashin amincewa da matasa wajen rike al'amurran jagoranci na siyasa.

KARANTA KUMA: Rundunar Sojin kasa ta damke wasu 'yan Kungiyar Asiri 23 da 15 masu Fashe Bututun mai a jihar Legas

Daya muhimmin abin kuma shine yadda ake ware matasa daga harkokin siyasa, zamantakewa da kuma tattalin arziki.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, binciken ya kuma tabbatar da yadda matasa kadan ke yin ruwa da tsaki cikin harkoki na tashi hankali yayin da mafi akasarin su ke gudanar da harkokin gaban su domin tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a zamantakewar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel