Sau biyar kawai na kwanta da diyar cikina – Inji wani Uba

Sau biyar kawai na kwanta da diyar cikina – Inji wani Uba

- Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 50, Taiwo Oyelabi, bisa ga laifin aikata zina da diyarsa

- Oyelabi wanda ke zama a unguwar Obadore, Iyana Oba, an zargeshi da yiwa diyar tasa ciki

- Wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da jami’an ‘Yan Sanda ke yi masa tambayoyi yace ‘sau biyar kadai ya kwanta da diyar tasa

Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 50, Taiwo Oyelabi, bisa ga laifin aikata zina da diyar cikinsa wadda a yanzu take da shekaru 21 a duniya.

Oyelabi wanda ke zama a gida mai lamba 15 community Road, a unguwar Obadore, Iyana Oba, a jihar Legas, an zargeshi da yiwa diyar tasa ciki.

Sau biyar kawai na kwanta da diyar cikina – Inji wani Uba
Sau biyar kawai na kwanta da diyar cikina – Inji wani Uba

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da jami’an ‘Yan Sanda ke yi masa tambayoyi yace ‘sau biyar kadai ya kwanta da diyar tasa’, amma ya nuna cewa itace ta fara nemansa da yayi lalata da ita bayan ta dawo gurinsa da zama daga hannun kanwarsa wadda mamarta ta barta a hannunta lokacin data bar gidansa.

KU KARANTA KUMA: Rahma Sadau ta caccaki Atiku Abubakar

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Legas Imohimi Edgal, a ranar Litinin lokacin da ya tasa keyar wanda ake zargin a helikwatarsu, yace binciken da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya kwanta da diyar tasa lokuta da dama.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Yan sanda sun kama wani mutumi mai shekaru 29, Soji Ogunrinola, bisa zargin yiwa yarinyar mai shekaru 13 fyade.

Yan sandan jihar Ogun ne suka kama mutumin wanda aka fi sani da bulldozer.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng