Hajj 2018: Kasar Saudi Arabiya na kokarin hana ‘yan Najeriya zuwa kasa mai tsarki
- Kasar Saudiyya na barazanar hana ‘yan Najeriya zuwa aikin hajjin bana
- Kasar Najeriya itace wadda tafi kowa yawan mahajjata, inda take da mahajjata a kalla 95,000
- Hukumar kula da mahajjata ta NAHCON ta bayyana cewa kasar ta Saudiyya tana barazanar ne akan barkewar cutar Lassa fever a Najeriya
Kasar Saudiyya na barazanar hana ‘yan Najeriya zuwa aikin hajjin bana. Kasar Najeriya itace wadda tafi kowa yawan mahajjata, inda take da mahajjata a kalla 95,000 a kowace shekara.
Hukumar kula da mahajjata ta NAHCON, a ranar Litinin ta bayyana cewa kasar ta Saudiyya tana barazanar ne akan barkewar cutar Lassa fever a Najeriya.
Dangane da rahotannin hukumar lafiya ta duniya (WHO), an samu mutane 1081 da ake zargin cutar ce ta kamasu sai kuma wasu 90 da suka mutu wadanda suma ana zargin cutar ce ta kashesu a jihohi 18 dake fadin Najeriya daga 1 ga watan Janairu zuwa 25 ga watan Fabrairu na wannan shekarar.
KU KARANTA KUMA: Rahma Sadau ta caccaki Atiku Abubakar
Daya daga cikin ma’aikatan hukumar NAHCON Mousa Ubandawaki, ya bayyanawa PREMIUM TIMES cewa kasar Saudiyya na barazanar hana mahajjatan Najeriya zuwa aiki bana, amma dai yace zasuyi taro da shuwagabanninsu na jihohin 36 da muke dasu a fadin kasar nan don samun mafita akan lamarin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng