An samu baraka a APC tsakanin magoya bayan Oshimole da na Oyegun

An samu baraka a APC tsakanin magoya bayan Oshimole da na Oyegun

- Sabon hatsaniya na neman ya shigo cikin Jam’iyyar APC a Najeriya

- Wasu manya a Jam’iyyar na tare da Shugaban yanzu John Oyegun

- Sai dai wasu kuma su na kokarin ganin Adams Oshiomole a kujerar

Mun samu labari cewa tsuguno ba ta kare ba a Jam’iyyar APC bayan da Shugabannin Jam’iyyar na Kudu-maso-kudancin kasar su ka musanya maganar da Gwamnan Jihar Edo Godswin Obaseki yayi kwanaki na marawa mai gidan sa baya.

An samu baraka a APC tsakanin magoya bayan Oshimole da na Oyegun
Magoya bayan John Oyegun sun ce zai iya sake takara

Mai girma Gwamnan ya nuna goyon bayan sa wajen ganin Adams Oshiomole ya samu kujerar Shugaban Jam’iyyar mai mulki sai dai wasu jiga-jigan APC a Yankin sun ce babu ruwan su da wannan magana kuma ba su amince da wannan ba.

Shugabannin Jam’iyyar APC na Jihohin Bayelsa, Kuros-Riba, Akwa-Ibom da ma Ribas sun ce ba su yi wa Adams Oshiomole mubaya’a ba. Wadannan shugabanni su ne Davies Ikanya, Deacon Joseph Fafi, Etim John da kuma Dr. Amadu Attai.

KU KARANTA: Masoyan Buhari sun gagara yin taro bayan Sanatan APC ya sha da kyar a Jihar Jigawa

Haka kuma wani babba a Jam’iyyar a Yankin na Kudancin kasar watau Victor Giadom yace ba su tare da Gwamna Obaseki a kan wannan batun. Kusoshin Jam’iyyar a Kudancin kasar sun ce an ari bakin su ne an ci masu tuwo amma ba su tare da Oshiomole.

Idan ba ku manta ba Legit.ng ta rahoto cewa Hilliard Eta ya bayyana cewa mutanen Yankin Kudu-maso-kudu sun tsaida Adams Oshimole a matsayin ‘Dan takarar su. Sai dai masu adawa da wannan sun ce matakin da aka dauka ba zai yi tasiri ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel