Rahma Sadau ta caccaki Atiku Abubakar
Shahararriyar jaruma wacce aka dakatar a dandalin shirya fina-finan Hausa, Rahma Sadau ta caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Hakan ya biyo bayan martanin da Atiku ya mayarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa matasan Najeriya ba cima zaune bane.
Ta zargi Atiku da cewa sune umul abaisin lalacewar matasan kasar musamman a yankunan Arewa. Cewa su suka maida matasa yan daba.
Ta kuma jadadda cewa sun kwana da sanin cewa Buhari masoyin matasan kasar ne.
Rahma Sadau ta aikewa da Atiku Martani kamar haka.
"Wai kana alfahari da matasa alhalin kune silar lalacewar matasan Najeriya musamman yankinmu na Arewa a lokacin mulkinku na PDP da kuka mayar da matasa yan daba kuna anfani dasu a matsayin karnukan farauta suna yin ta'addanci kala kala dan ku samu mulki ko ta wani hali.
“Mu mun san Buhari masoyin matasan Nigeria ne dan haka matasa kada ku yadda wani dan jari hujja ya yaudareku. 2019 sai Baba insha Allah" Inji Rahama Sadau.
KU KARANTA KUMA: Ba gaskiya ba ne Mai martaba yace na guji taro a Birtaniya don wani aiki ya kai mu Amurka - Kachiwku
A halin da ake ciki ana ci gaba da cece-kuce akan furucin da shugaban kasa Buhari yayi game da matasan Najeriya a kasar Ingila.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng