Babban kalubalen da na fuskanta a aiki karkashin Jonathan - Ministar kudi Ngozi Okonjo Iweala
Tsohuwar Ministan Kudi, Ngozi Okonjo-Iweala ta bayyana babban kalubalen da ta fuskanta a lokacin da ta yi aiki karkashin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Minsitar na yin wannan waiwaye ne a cikin wani littafi da ta wallafa cikin harshen turanci mai suna 'akwai hatsari a cikin yaki da cin hanci."
Ngozi ta ce, dangantakar ta da ma'aikatan kamfanin mai na kasa (NNPC), shine babban kalubalen ga ofishinta. A cewar ta, rashin fayyace komai a harkar gudanarwa daga kamfanin mai na kasa NNPC, da kuma ma'aikatar albarkatun mai, babbar matsala ce da take kassara cigaban kasar nan.
A cikin littafin nata, Tsohuwar Ministan Kudi ta rubuta cewa, binciken da ma'aikatar ta ta gudanar, ya nuna ana samun gibin Naira Bilyan 160 duk shekara, wanda kamfanin mai na kasa NNPC ya bayyana haka da cewar, na faruwa ne sakamakon barayin dake fasa bututun mai.
DUBA WANNAN: An gurfanar da dan shekara 40 da ya yiwa wasu daliban firamare uku fyade a Katsina
Okonjo-Iweala ta ce, ta sha wuya sosai a kokarinta na kawo sauyi don fito da komai fili a harkar gudanar dakamfanin mai na kasa daga ma'aikatan kamfanin. "Zan iya cewa shine aikin da ya fi kowanne wahala da kasada a aikina na mmnistan kudi" In ji tsohuwar ministan kudin a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng