Zamba cikin aminci: wata Mata mai shekaru 39 ta saci jaririyar makwabciyarta

Zamba cikin aminci: wata Mata mai shekaru 39 ta saci jaririyar makwabciyarta

Daga bata ajiya don yin lallashi, wata Mata mai shekaru 39, Fausat Hammed ta sace wata jaririya yar wata biyu a Duniya a ranar 16 ga watan Afrilu, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

A ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu ne jami’an Yansanda suka gurfanar da matar a gaban Kotun majistri dake Unguwar Ebute Meta na jihar Legas don amsa laifinta, kamar yadda majiyar Legit.ng.

KU KARANTA: Jerin fitattun lauyoyi guda 64 da suka samu lambar kwarewa ta SAN

Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Chinalu Uwadione ya bayyana cewa wanda ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Afrilu a gida mai lamba 49, layin Giwa, unguwar Ijora-Badia dake jihar Legas.

Dansandan ya bayyana cewar an baiwa Fausat ajiyan jaririyar ce, daga nan ta yi awon gaba da jaririyar, a kokarinta na sace ta, wanda yace laifin yaci karo da sashi na 275 na kundin hukunta manyan laifuka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito laifin na dauke da hukuncin zaman Kurkuku na shekaru 14, kamar yadda kundin hukunta manyan laifuka ta tanadar.

Sai dai Fausat ta musanta aikata laifin, daga nan kuma Alkalin Kotun, mai shar’a O.A Adegite ta bada belinta akan kudi Naira dubu dari hudu, N400,000 tare da mutane biyu da zasu tsaya masa, daga nan kuma ta dage sauraron karar zuwa 23 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng