Kada ka sake ka amince da shawarar halasta auren jinsi ɗaya a Najeriya - CAN

Kada ka sake ka amince da shawarar halasta auren jinsi ɗaya a Najeriya - CAN

- Musulmai da Kirista an zama daya wajen rashin amincewa da tayin halasta auren jinsi

- Kungiyar CAN tace, sun yarda Buhari ba zai amince ba, amma ko nan gaba wata gwamnati tazo to ga matsayinta ta fada

Kungiyar Kiristoci ta ƙasa (CAN) ta shawarci gwamnatin Shugaba ƙasa Muhammadu Buhari da tayi watsi da tayin halasta auren jinsa ɗaya da Firaministan Ingila Theresa May tayi masa.

Wannan shawara na kunshe ne cikin jawabin Pasto Adebayo Oladeji, mataimaki akan harkokin yaɗa labarai na shugaban ƙungiyar na ƙasa Dr. Olasupo Ayokunle.

Kada ka amince da shawarar halasta auren jinsi ɗaya a Najeriy - CAN
Kada ka amince da shawarar halasta auren jinsi ɗaya a Najeriy - CAN

Idan ba'a manta ba, Firaministar ta yiwa shugaba Buhari tayin amincewa da halasta auren jinsi a Najeriya yayin taron ƙasashe rainon Ingila. An dai rawaito tana cewa bai kamata a samu wata doka da zata riƙa ɗaukar masu ɓukatar auren jinsi ɗaya a matsayin masu laifi a ƙasashen rainon Ingilar.

Shugaban ƙungiyar kiristocin ta ƙasa ya ƙara da, "Abinda Firaminita Theresa take so ayi ya saɓa da umarnin ubangiji, kuma hanya ce ɗoɗar ta gamuwa da shaiɗan wacce bai kamata a goya mata baya ba sai dai ma mutane masu tunani su juya mata baya a duk duniya, musamman a Najeriya".

A cewarsa, ƴan Najeriya tuntuni sun haɗu akan cewa basa goyon bayan mummunar halayyar ta aure tsakanin jinsi guda, a saboda haka yan Najeria ba za su ajiye rayinsu su ɗauki shawarar ta ta ba.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi ram da manyan ‘Yan Boko Haram 2 a Borno

"Idan mahukuntan Ingila sun manta sai mu tuna musu, wannan batun na aure tsakanin jinsi guda ya saɓawa addinanmu (Littattafai), kuma duk wata dokar da Mutum ne ya kafa ta mutuƙar ta saɓa da Littafi mai tsarki to ba abar bi ba ce".

"Ubangiji ne ya shari'anta ayi aure kuma ya faɗi yadda yake so ayi ƙarara cewa Namiji ya auri Mace a cikin littafin (Genesis 2:24). Kuma mai cetonmu Yesu Almasihu yace Aure ayi shi tsakanin Mace da Namiji (Mathew 19:4). Littafin Bible ya la'anci aure tsakanin jinsi da cewa babba zunubi ne Leviticus 18:22. Shugaban ya jaddada.

"Matsayin CAN akan wannan batun shi ne, duk wata gwamnatin da ta yarda da wannan batun na aure tsakanin jinsi, tamkar tayi shirin yin fito na fito ne da Ubangiji, kuma mu ma Kirista a kasar da saura jama'a ba za mu zuba mata ido ba balle mu goyi bayanta".

Don kasar Ingila ta yarda da shi da sauran wasu ƙasashen, hakan ba zai halasta shi ba.

Kada ka amince da shawarar halasta auren jinsi ɗaya a Najeriy - CAN
Kada ka amince da shawarar halasta auren jinsi ɗaya a Najeriy - CAN

ya cigaba da fadin, duk wani umarni da ya saɓawa umarnin Ubangiji to CAN da sauran ƴan Najeriya baza su taɓa amince da shi ba. Kuna ya kamata ita firaministar ta ɗauki darasi daga wurin dabbobi, su da suke marasa tunani ma har yanzu aure tsakanin jinsi daba-daban suke yi balle mu mutane.

"Auren jinsi shi ne dalilin da yasa aka kifara da Mutane Soom da Gomorrah a cikin Bible yana nan labarin. Babu wata doma ta ƴancin ɗan Adam da zata jingine dokar Ubangiji".

Shugaban ƙungiyar ya cigaba da cewa, kada wani dalili ko matsin lamba ya sanya gwamnatin Najeriya tunanin amincewa da shi. Kuma Najeriya ƙasa ce mai cikakkiyar iko zartar da dokokinta ba tare da anyi mata katsalandan ba.

Tun a wurin taron ne Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya maryarwa da Firaministar martani nan take ba tare da barin ta huce ba, inda yace, Najeriya bata da ra'ayin amincewa da irin wannan doka domin auren jinsin ya saɓa da addini d al'adar mutanen Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng