Turnuku fadan ifiritai: 'Yan sandan Najeriya sun gabza fada da dodanni, sun kama 3

Turnuku fadan ifiritai: 'Yan sandan Najeriya sun gabza fada da dodanni, sun kama 3

Mahukunta a rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Anambra sun sanar da samun nasarar da suka yi akan wasu dodanni da suka hargitsa ayyukan ibada a wata majami'ar dake a karamar hukumar Idemili ta yamma a ranar Juma'ar da ta gabata da dare.

Jami'ar hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan ne dai Nkeiruka Nwode ta shaidawa manema labarai hakan a garin Awka, babban birnin jihar.

Turnuku fadan ifiritai: 'Yan sandan Najeriya sun gabza fada da dodanni, sun kama 3
Turnuku fadan ifiritai: 'Yan sandan Najeriya sun gabza fada da dodanni, sun kama 3

KU KARANTA: Gwamnoni 5 da ake sa ran su yi tazarce a 2019

Legit.ng ta samu cewa Uwar gida Nkeiruka Nwode ta kuma kara da cewa jami'an su sun samu nasarar kama wasu uku daga cikin dodannin kuma tuni ma har bincike a kan su yayi nisa.

A wani labarin kuma, Akalla mutane uku ne ciki hadda babban malamin addinin kirista suka rasa ransu a wajen taron tattaunawa na jam'iyyar APC mai mulki a jihar Benue dake a shiyyar Arewa ta tsakiya, ranar Juma'ar da ta gabata a garin Otukpo.

Wakilin majiyar mu dai ya bayyana mana cewa jim kadan bayan fara taron ne sai fada ya barke a tsakanin mabiya bangarori biyu da basu ga maciji da juna na shugaban jam'iyyar na jiha da kuma wani dan majalisar tarayya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel