Sabuwar cutar tsutsa ta bulla a gonaki a Kebbi, manoma na fargabar bazuwarta

Sabuwar cutar tsutsa ta bulla a gonaki a Kebbi, manoma na fargabar bazuwarta

- Manoma a jihar Kebbi sun sanar da yanda tsutsa suka fadawa albarkatun gonar su, suke lalacewa

- A rahoton da daily trust ta samo na manoma, a kwanakin baya ne kwari suka sa albarkatun gonar su gaba a jihar

- Manoma da masana a ma'aikatar aikin gona suna cigaba da nemo mafita

Sabuwar cutar tsutsa ta bulla a gonaki a Kebbi, manoma na fargabar bazuwarta
Sabuwar cutar tsutsa ta bulla a gonaki a Kebbi, manoma na fargabar bazuwarta

A ziyarar da ya kai gonakin da ya shafa, majiyar tamu, ta samu kwarin sunyi barna a gonaki musamman na Zuru, Argungun, Bunza, Bagudo, kamba, birnin Kebbi da sauran gurare na jihar.

Wannan dai ya zama abin damuwa ga manoman yankin, manoma sunce duk da yawan ruwan da ake zukowa zuwa gonakin a kullum, shukokin sun bushe sakamakon tsutsotsi da suke cin su.

A sakamakon haka gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu ya kai ziyara ga gonakin da abin yafi shafa. A zuwan da yayi matankari ta karamar hukumar Suru, Alhaji Umaru Maigandi Dakingari, shugaban karamar hukumar Suru ya zagaya da gwamnan gonakin da abun ya shafa.

Duk da Gwamna Bagudu yaso ya kwantar da hankalin manoman ta hanyar tabbatar musu cewa Gwamnatin jihar zata hada guiwa da gwanatin tarayya don magance tsutsotsin, damuwar manoman ta bayyana.

DUBA WANNAN: Mun gama fa da Boko Haram - Buratai ya fadi wa duniya

Daya daga cikin manoman da abin ya shafa yace "Ban taba ganin Abu makamancin haka ba a cikin shekara 20 da nayi ina noma.

Mutane da yawa bazasu yarda ba Idan aka fada mishi irin barnar da tsutsotsin sukayi" "inji Alhaji Abdulwasi'u Andarai. Manomin yayi kira ga Gwamnatin jihar da su kawo taimakon gaggawa tun kafin rashin abinci ya tabbata a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng