Yanzu Yanzu: Wata ‘yar Najeriya ta kara samun babban matsayi a majalisar dinkin duniya

Yanzu Yanzu: Wata ‘yar Najeriya ta kara samun babban matsayi a majalisar dinkin duniya

- Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya tabbatar da nada Bola Adesola na Najeriya cikin shuwagabannin majalissar dinkin duniya

- Tsohuwar Minista a Najeriya Amina Mohammed itace mataimakiyar Sakatare Janar na majalisar ta dinkin duniya

- Ms. Adesola atre da Mr. Polman sune zasu maye gurbin Sir Mark Moody-Stuart, tsohon ciyaman na Royal Dutch/Shell Group of Company da kuma Anglo American plc

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya tabbatar da nada Bola Adesola na Najeriya cikin shuwagabannin majalissar dinkin duniya, a jawabin damajalissar ta fitar a kasar New York a ranar Juma’a.

Tsohuwar Minista a Najeriya Amina Mohammed itace mataimakiyar Sakatare Janar na majalisar ta dinkin duniya.

Ms. Adesola atre da Mr. Polman sune zasu maye gurbin Sir Mark Moody-Stuart, tsohon ciyaman na Royal Dutch/Shell Group of Company da kuma Anglo American plc.

Babban Sakataren ya mika godiyarsa ga Sir Mark bisa ga aikin da yayiwa majalisar na tsawon shekaru goma.

Yanzu Yanzu: Wata ‘yar Najeriya ta kara samun babban matsayi a majalisar dinkin duniya
Yanzu Yanzu: Wata ‘yar Najeriya ta kara samun babban matsayi a majalisar dinkin duniya

Ms. Adesola ta rike matsayin babbar ma’aikaciya da kuma Manajan Darakta a bankin Standard Chartered Bank Nigerian Ltd a shekarar 2011.

Ta samu horo na shekaru 25 a aikin banki wadanda suka hada da First Bank da Citibank, tana kuma da Digiri a fannin kasuwanci daga jami’ar Havard da kuma makarantar kasuwanci ta jihar Legas, sannan kuma ta samu Digiri a fannin Lauyanci daga jami’ar Buckingham.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta damu da cigaban matasa - Ministan Buhari

Mr Polma na kasar Netherlands, wanda ya kasance shine babban ma’aikacin zartarwa na Unilever tun a shekarar 2009, wanda kafin nan yayi aiki da Nestle S.A da kuma Proctor and Gamble, inda yayi shekaru 26. Mr. Polma ya samu Digiri daga jami’ar Groningen da kuma jami’ar Cincinati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel