Ka janye maganarka sannan ka ba matasan Najeriya hakuri – Shehu Sani ya shawarci Buhari

Ka janye maganarka sannan ka ba matasan Najeriya hakuri – Shehu Sani ya shawarci Buhari

Sanata Shehu Sani yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ba matasan Najeriya hakuri kan furucin da aka ce yayi na cewa matasan Najeriya yan cima-zaune ne.

Sanatan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a 20 ga watan Afrilu inda ya bukaci shugaba Buhari da ya janye kalaman nasa.

Ya kara da cewa shugaban kasar ya fadawa matasa abunda yayi masu da kuma wanda zaiyi masu a nan gaba.

Ka janye magananka sannan ka ba matasan Najeriya hakuri – Shehu Sani ya shawarci Buhari
Ka janye magananka sannan ka ba matasan Najeriya hakuri – Shehu Sani ya shawarci Buhari

KU KARANTA KUMA: Manyan Najeriya 3 da saudiyya ta karrama ta hanyar bude masu ka'aba

A halin da ake ciki, shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da shan caccaka bayan jawabin da yayi a kan matasan Najeriya a kasar Ingila.

Kalaman ya fusata matasa da dama sannan kuma ya ba masu adawa da shugaban kasar damar tofa albarkacin bakinsu inda suke ci gaba da tunzura matasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng