Gwamnatin Tarayya za ta bada aikin hanyar Bida har zuwa Lambata
- Za a gyara hanyar nan ta Garin Bida zuwa Lapai a cikin Jihar Neja
- Doguwar Hanyar ce ta hada Kudu maso yamma da Arewacin kasar
- Za a kashe sama da Naira Biliyan 30 wajen wannan gagrumin aiki
Mun samu labari cewa a makon nan ne Gwamnatin Tarayya ta amince za ta bada aikin hanyar Garin Bida da ya dauko zuwa Lapai ya kuma tike zuwa Garin Lambata a cikin Jihar Neja wanda zai ci sama da Naira Biliyan 30.
An yi zaman Ministoci na mako-mako da aka saba a fadar Shugaban kasa wanda Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta. A zaman na wanna makon an amince za a gyara hanyar Bida zuwa Lambata
KU KARANTA: Ba za mu iya kada APC ba gaskiya - APC
Tsawon titin ya kai kilomita 120 kuma shi ne titi na biyu da ya hada Arewa sa Kudancin Kasar. Bayan haka kuma an amince a kashe Biliyan 6 domin sayen wasu kayan jirgi a filayen Legas da Benin da na Garin Akure.
Mustafa Baba Shehuri wanda shi ne karamin Ministan ayyuka na kasar ya bayyana wannan lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da wasu Ministoci a fadar Shugaban kasar. Za a kashe Biliyan 33 inji Ministan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng