Kotu ta bayar da belin yan Shia 22 da aka tsare

Kotu ta bayar da belin yan Shia 22 da aka tsare

Wata kotun Majistare dake Abuja ta bayar da belin yan shia 22 da aka tsare a ranar Alhamis, 19 ga watan Afrilu.

Yan sanda ne suka kama yan shian a ranar Litinin sannan kuma aka zarge su da ta’addanci, taro ba bisa ka’ida ba, tada zaune tsaye, da sauransu.

Haka zalika an kama kakakin kungiyar kare hakkin biladam, da yan Najeriya da suka taya yan shian yin zanga-zangan a saki shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky.

Daga cikin aka gurfanar a gaban mai shari’a, Yusuf Ubangari, da wasu yara uku. Ga mutanen uku, kotu ta bayar da belinsu kan N300,000 da sanya hannun iyayensu ko masu kula dasu.

Kotu ta bayar da belin yan Shia 22 da aka tsare

Kotu ta bayar da belin yan Shia 22 da aka tsare

Kakakin kungiyar yan Najeriya masu kishi, Theophilus Agagda, ma ya samu beli na N300, 000 sanya hannun jami’in gwamnati mai matsayi akalla mataki na takwas sannan kuma ya kasance yana zama a kewayen kotun.

KU KARANTA KUMA: 2019: Bazamu iya kada APC ba idan bamu hada kawunan mu ba - PDP

Haka ma an bayar da belin sauran 19 kan matsaya guda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel