Kamfanin Shell zai saka hannun jarin Dala Biliyan 15 a Najeriya - Shugaba Buhari

Kamfanin Shell zai saka hannun jarin Dala Biliyan 15 a Najeriya - Shugaba Buhari

- A jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari yace kamfanin shell na shirye shiryen saka hannun jari na dala biliyan 15 a Najeriya

- Shugaban ya bayyana hakan ne a taron kasuwanci na Commonwealth a Guildhall, Landan inda ya bukaci dangantakar kasuwanci mai kyau tsakanin kasashen Commonwealth

Kamfanin Shell zai saka hannun jarin Dala Biliyan 15 a Najeriya - Shugaba Buhari
Kamfanin Shell zai saka hannun jarin Dala Biliyan 15 a Najeriya - Shugaba Buhari

A jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari yace kamfanin shell na shirye shiryen saka hannun jari na dala biliyan 15 a Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a taron kasuwanci na Commonwealth a Guildhall, Landan inda ya bukaci dangantakar kasuwanci mai kyau tsakanin kasashen Commonwealth.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC zata gurfanar da Sanata Kwankwaso da Wamako

"Kafin inzo wannan taron, kungiyar shell sun zo sun sanar dani suna shirye shiryen saka hannun jarin dala biliyan 15 a Najeriya." inji shugaba Buhari.

Shugaban yace dole kasashen Commonwealth su guji fadan cinikayya kuma muyi aiki tare don cimma burikanmu.

A wata zantawa da mai magana da yawun shugaban kasan Mista Femi Adesina yace shugaban yace kasashen yan kungiyar Commonwealth din su dage da tallafawa juna don hadin kan bangarori. Ya nuna cewa cinikayya da zuba hannayen jari hanyoyin samun cigaba ne abin dogaro, saukin yin kasuwanci da hadin kan bangarori. Ya kara da cewa tallafawa mata da samari hanyoyi ne na habaka kasuwanci.

Shugaba Buhari yayi kira ga taron kasuwanci na Commonwealth da kuma masu hannun jari a Najeriya dasu taka rawar gani a taron cinikayya da hannun jari na 2018 tsakanin UK da Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng