Matasan Najeriya sun wuce a kira su da cima-zaune - Abubakar Sani

Matasan Najeriya sun wuce a kira su da cima-zaune - Abubakar Sani

Shahararen mawakin nan na Hausa, Abubakar Sani yayi sharhin akan furucin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi game da matasan Najeriya a kasar Ingila.

Acewar Abubakar, matasan kasar sun wuci a kirasu da cima-zaune.

Ya kalubalanci shugaban kasar day a shiga wajajen koyon sana’o’in hannu da kasuwanni ya ga yanda maza da mata ke tururuwa wajen baje kwanjinsu.

Ya kuma kalubalanci matasa da suyi la’akari da wanda ke son su ba wai wanda su suke so ba.

Matasan Najeriya sun wuce a kira su da cima-zaune - Abubakar Sani

Matasan Najeriya sun wuce a kira su da cima-zaune - Abubakar Sani

Ya yi jawabi kamar haka: “Tabbas yanzu na kara jaddada cewa wannan gwamnatin ta Najeriya ba ta talakawa bace kuma ba ruwanta da matasa. Ya za ka dubi matasan kasar nan kace musu cima zaune?

KU KARANTA KUMA: APC ta roki Buhari akan ya bawa matasan Najeriya hakuri game da maganganu da yayi akansu

“Ka shiga kasuwanni, ka shiga makarantu, ka je guraran sana'o'in hannu irin su gine-gine, kafinta, dinki, gayran mota, kai ka je guraren sai da abinci duk da sana'ar mata ce amma yanzu maza da mata ne suke yinta, Kuma matasa.

“Dan haka matasa kalubale akan mu, sai mu canja da wanda yake san mu ba wanda muke so ba.”

A kwanakin baya Legit.ng ta kawo inda Abubakar Sani ya nuna adawarsa da sake takaran da shugaba Buhari ya kuduri yi a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel