Matasa sun mayar da martani ga shugaba Buhari akan batun lalaci da cima zaune

Matasa sun mayar da martani ga shugaba Buhari akan batun lalaci da cima zaune

Da yawan al'ummar Najeriya musamman matasa sun tayar da jijiyoyin wuya a yayin da suke mayar da martani ga kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari na ranar Larabar da ta gabata da malalata ne kuma cima zaune.

Matasa sun mayar da martani ga shugaba Buhari akan batun lalaci da cima zaune
Matasa sun mayar da martani ga shugaba Buhari akan batun lalaci da cima zaune

Shugaban kasa Buhari a yayin jawaban sa na birnin Landan da ya gudanar a taron kasashe masu cin gashin kansu ya bayyana cewa, Najeriya tana da kimanin al'umma miliyan 180 wanda kaso 60 cikin 100 matasa ne kuma mafi akasarin su marasa ilimi 'yan cima zaune.

KARANTA KUMA: Ba mu da masaniya akan shirin 'yan Shi'a na kai hari garin Abuja - Gwamnatin Tarayya

A yayin da wasu matasan suka mayar da martani dangane da kalaman shugaban kasar, wasun su sun bayyana yadda 'yan uwan su matasa ke gwagwarmaya ta neman na kansu ba tare da dogaro ko neman tallafin gwamnati ba.

Matasan sun kuma nemi shugaba Buhari akan ya daure wajen cika alkawurran da ya dauka a yayin yakin neman zaben na cewar zai samar da aikin yi.

Ga wasu daga cikin martanin da Matasan suka yiwa shugaban kasa:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng