Kalaman Shugaba Buhari sun jawo fushin Matasa a Najeriya
- Jawabin da Shugaban kasa Buhari yayi a Landan sun bar baya da kura
- Shugaba Buhari yace yawancin Matasan kasar ba su da kwazo sai lalaci
- Wasu Matasa sun maida martani inda su kace su fa ba ci-ma-zaune bane
Shugaba Buhari yayi kaca-kaca da Matasan Najeriya inda yace wasu ba su sa komai a gaba ba sai lalaci. Wannan magana ta Shugaban kasar ta fusata matasan kasar da Gwamnatin APC tayi wa alkawarin samawa aiki..
Shugaban kasa Buhari yace da dama na Matasan kasar ‘yan kashe wando ne da ci ma zaune da kuma zaman banza inda su ke jira Gwamnati tayi masu komai ba tare da sun mike ba. Da dama dai sun fito sun yi tir da wannan magana.
KU KARANTA: Gwamnatin Shugaba Buhari ta nemi a janye yajin aiki
Wani babban Masani a kasar Dr. Aminu Gamawa yayi tir da wannan kalamai inda yayi kira ga Shugaban kasar ya rika tauna kalaman sa saboda gudun ayi masa mummunan fassara. Matasa a kasar dai sun ce ba za a kira su kasalallu ba.
Wani Bawan Allah ya koka da jawabin na Shugaba Buhari inda yace wannan Gwamnati ta kashe tattalin arziki sannan kuma Matasa da dama sun rasa aikin su. Ana dai zargin Gwamnatin Buhari ba ta bada aiki sai ga masu kafa a kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng