Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun saki Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege

Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun saki Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege

- Sanata Ovie Omo- Agege wanda ake zargi da shiga cikin majalisa ba tare da bisa ka’ida ba, ya samu sake daga hukumar ‘Yan Sanda

- Sanatan ya samu sake daga hannun hukumar ta ‘Yan Sanda bayan yayi masu bayanin dalilin shiga majalissar ba bisa ka’ida ba tare da ‘yan ta’adda

- Sanatan ya gardanta yiwa ‘yan ta’addan jagoranci zuwa shiga majalissar kuma ya gardanta cewa shi ya dauki sandar girman ta majalissa ya bawa ‘yan ta’addan

The Nation ta bayyana cewa Sanata Ovie Omo- Agege wanda aka zarga da shiga cikin majalisa ba bisa ka’ida ba, ya samu sake daga hukumar ‘Yan Sanda.

Bayanin da ya fito daga Ofishin Sanatan mai wakiltar jihar Delta ta cikiya ya tabbatar da cewa, Omo-Agege ya samu sake daga hannun hukumar ta ‘Yan Sanda bayan yayi masu bayanin dalilin shiga majalissar ba bisa ka’ida ba tare da ‘yan ta’adda.

Sanata ya gardanta yiwa ‘yan ta’addan jagoranci zuwa shiga majalissar, kuma ya gardanta cewa shi ya dauki sandar girman ta majalissar ya bawa ‘yan ta’addan.

Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun saki Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege

‘Yan Sanda sun saki Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege

Wani bayan daya fito daga bakin lauyoyin majalissar Barrister Lucky Ajos yace “Sanata Omo-Agege yaje aiki a yau kamar yadda kowane Sanata ke zuwa aiki; bai dauke Sandar Girma ta majalissar ba bayan majalissar ta dakatar dashi a ranar 12 Alhamis 12 ga watan Afirilu 2018.

KU KARANTA KUMA: Matan Chibok: ‘Yan Boko Haram sun gaskata Ahmad Salkida

Bayan haka kuma Sanatan yau yaje aiki kamar kowane sanata ya kuma zauna tare da abokanan aikinsa a majalissar”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel