Ba mu da masaniya akan shirin 'yan Shi'a na kai hari garin Abuja - Gwamnatin Tarayya
Da sanadin shafin jaridar Daily Trust, mun samu rahoton cewa gwamnatin tarayya ta yi watsi da jita-jitar da ke yaduwa a kafofin dandalan sada zumunta da cewar kungiyar 'yan shi'a ta Najeriya watau IMN na shirye-shiryen kai hari garin Abuja.
Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labari na fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar ministoci da suka gudanar na ranar Talatar da ta gabata.
Ministan ya bayyana cewa, ba ya da masaniyar tushen wannan jita-jita, inda ya janyo hankalin 'yan najeriya akan gujewa kanzon kurege dake yaduwa a dandalan sada zumunta.
KARANTA KUMA: Ka ceto 'yan Matan Chibok da Leah kafin zaben 2019 - Majalisar Wakilai ga Shugaba Buhari
A kalaman Dambazau, "ku kasance masu lura wajen tace rahotonni masu inganci, kuma ko shakka babu ina da tabbacin doka da oda a cikin al'umma."
Ya kara da cewa, "Ministan birnin tarayya da kwamishinan 'yan sanda suna zaune cikin shirin duk wani abu da zai kai koma a birnin."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng