Matan Chibok: ‘Yan Boko Haram sun gaskata Ahmad Salkida
- Wani Sojan Boko Haram yace yaran Chibok 30 ne kurum ke kasa
- Kwanakin baya dai wani ‘Dan jarida yace wasu matan sun mutu
- Yanzu haka ana fafatukar a maido ‘Yan matan da aka sace a baya
Kwanakin baya wani fitaccen ‘Dan jarida mai bincike game da Boko Haram watau Ahmed Salkida ya bayyana cewa da dama cikin ragowar ‘Yan matan Chibok ba su da rai a halin yanzu yayin da wasu kuma su ke auren ‘Yan ta’addan.
Dazu nan mu ka samu labari daga wata Kungiya mai zaman kan-ta dage binciken kwa-kwaf a Kasashen Duniya inda ta bayyana cewa maganar da Salkida yayi babu tantama a cikin ta yayin da ake bikin cika shekaru 4 da sace yaran.
KU KARANTA: Sababbin Malaman Jihar Kaduna sun soma aiki
Ahmed Salkida ya bayyana cewa wani Sojan Boko Haram ya tabbatar masa da cewa wasu 10 daga cikin ‘Yan matan na Chibok da aka sace su na tsare. Bayan nan kuma akwai wasu mata akalla 15 su na auren Sojojin’Yan ta’ddan yanzu.
Yanzu dai cikin ragowar ‘Yan matan da aka sace kusan 30 ne kurum ke da rai. Shi dai Salkida a baya yace yara 15 ne kacal su ka rage. Wani babba a Kungiyar ta Jama’atu Ahlis-Sunna Lidda’Awati Wal-Jihad dai yayi karin haske.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng