Ban taba cewa ina kyamar masu soyayyar jinsi daya ba - Ministan Wuta Fashola

Ban taba cewa ina kyamar masu soyayyar jinsi daya ba - Ministan Wuta Fashola

- Kurkukun shekara 14 saboda soyayyar jinsi daya a Najeriya

- Fashola ya karyata cewa shima yana kyamar su

- Jonathan ne yayi dokar bisa soyayyarsa ga coci da Fastoci

Ban taba cewa ina kyamar masu soyayyar jinsi daya ba - Misistan Wuta Fashola
Ban taba cewa ina kyamar masu soyayyar jinsi daya ba - Misistan Wuta Fashola

Tun bayan da shugaba Jonathan ya rattaba han kan dokar da majalisar dattijai ta zamaninsa ta iyar, na gallazawa wadanda basu ji ba basu gani ba, kawai don suna son juna, abu da bai shafi gwamnati ba, domin ya farantawa coci da limamanta, ake kara nuna kyama ga masu halayyar.

Su dai masu son juna a jinsi daya, watau LGBT, wanda sun hada da masu luwadi, madigo da ma wadanda ke tsakiya, kamar 'yan daudu da mata-maza.

A kimiyyance dai, an fahimta halitta ce da ta shafi sinadarai dake yawo cikin jini, musamman Oestrogen da Testestherone, amma malaman addinai da basu yi biology ba suke zuba fatawa akai, har da zuga gwamnati tayi dokar kurkuku shekaru 14 a kulle.

DUBA WANNAN: An saki wani bidiyo kan Buhari da ba lallai yayi wa gwamnatin dadi ba

A taron da ake yi yanzu haka a Ingila, Ministan ayyuka na Najeriya, Babatunde Raji Fashola, ya wanke kansa kan batun ayan da aka yi masa tambaya ko yana kyamar irin wadannan mutane masu soyayyar jinsi.

"Ban taba cewa ina kyamar masu soyayyar jinsi daya ba, ko yanzu, ko sanda ina gwamna a jihata ta Legas." ya fadi a taron Commonwealth Peoples Forum na Commonwealth Head of Governments Meeting (CHOGM 2018) a Westminster.

Firai Ministar Ingilar, Theresa May, tayi kira ga gwamnati da ta cire dokar daga aiki, domin a cewarta, babu wani laifi muddin kawai masu soyayya ne ke lobayyarsu, ku maza ko mata.

Babu dai alamar shugaba Buhari zai iya sauya wannan doka, musamman ganin yawancin mutanen Najeriya addinai ke gaya musu alkibla, ba wai ilimin kimiyya ko fahimtar duniya ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel