2019: ‘Yan Kasuwa a jihar Buhari sunce zasu siyawa shugaban kasa da Masari fom din sake tsayawa takara

2019: ‘Yan Kasuwa a jihar Buhari sunce zasu siyawa shugaban kasa da Masari fom din sake tsayawa takara

- Kungiyar hade-haden ‘yan kasuwa a jihar katsina tace zata siyawa Shugaban kasa Buhari da Gwamna Aminu Masari Form na sake tsayawa takara a zaben 2019 mai zuwa

- Ibrahim Dikko mai magana da yawun kungiyar yace kungiyar tasu tana da kananan kungiyoyi 70, sannan suna da Ciyaman da kuma ma’aikata a kananan hukumomi 34 na jihar

- Ibrahim yace sunyi shawarar siyawa shugaba Buhari da gwamna Masari form dinne sakamakon ayyukan alkhairi da suke ta aiwatarwa da kuma cigaban da suke ta kawowa a fannonin ayyukansu

Kungiyar hade-haden ‘yan kasuwa a jihar katsina tace zata siyawa Shugaban kasa Buhari da Gwamna Aminu Masari Form na sake tsayawa takara a zaben 2019 mai zuwa.

Ibrahim Dikko mai magana da yawun kungiyar yace kungiyar tasu tana da kananan kungiyoyi 70, sannan suna da Ciyaman da kuma ma’aikata a kananan hukumomi 34 na jihar, ya bayyana hakane lokacin da suka kaiwa Masari ziyara a gidan gwamnatin jihar katsina.

Kungiyar wadda Bala Usman Zango, mai bawa gwamna shawara ta fannin al’amuran siyasa, ya jagoranta lokacin ziyayar.

Ibrahim yace sunyi shawarar siyawa shugaba Buhari da gwamna Masari form dinne sakamakon ayyukan alkhairi da suke ta aiwatarwa da kuma cigaban da suke ta kawowa a fannonin ayyukansu, musamman ta fannin tsaro.

KU KARANTA KUMA: Babu makawa Atiku zai kora Buhari Daura - Hadiminsa

Ya kuma kara da cewa suna kokarin kaddamar da kamfen ne a jihar ta katsina, don fadawa mutane cewa su zabi shugaba Buhari da Masari a zaben 2019 mai zuwa, yace musamman ma mutanen dake cikin kauyuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel