Da dumi: Uwargidan tsohon Shugaban kasar Amurka ta riga mu gidan gaskiya

Da dumi: Uwargidan tsohon Shugaban kasar Amurka ta riga mu gidan gaskiya

Rahotannin safiyar yau Laraba da sanadin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, Barbara Bush, matar tsohon shugaban kasar Amurka ta riga mu gidan gaskiya kamar yadda kakakin danginta, Jim McGrath ya bayyana a ranar Talatar da ta gabata.

Tsohon shugaban kasa W.H. Bush tare da marigayiya Barbara

Tsohon shugaban kasa W.H. Bush tare da marigayiya Barbara

Barbara a yayin rayuwarta ta kasance matar tsohon shugaban kasar Amurka, George H. W. Bush, da rike karagar mulkin kasar a tsakanin shekarar 1989 zuwa 1993 ya kasance shine shugaban kasar na 41 kamar yadda tarihin ta ya bayyana.

KARANTA KUMA: Babbar Magana: Ma'aikatan Lafiya za su shiga Yajin Aiki na sai Mama ta gani

Marigayiya Barbara ta kuma kasance mahaifiya ga tsohon shugaban kasar na 43, George W. Bush kuma mahaifiya ga gwamnan jihar Florida na 43, Jeb Bush.

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Punch sun bayyana cewa, Barbara ta riga mu gidan gaskiya ne tana da shekaru 92 a duniya, bayan ta auri mijinta shekaru 73 da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel