Sai mun yaki cin hanci da rasahawa da kuma amfani da miyagun kwayoyi – Ibrahim Maishinku

Sai mun yaki cin hanci da rasahawa da kuma amfani da miyagun kwayoyi – Ibrahim Maishinku

Shahararren jarumin nan na kamfanin shirya fina-finan Hausa Kannywood, Ibrahim Maishinku yayi ikirarin cewa zasu taka rawar ganinsu wajen ganin sun magance matsalar cin hanci da ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar.

Maishinku ya bayyana hakan ne a wajen taron da kungiyoyi na jihar Sokoto, a zagayen jihohin da suke domin yekuwa da aka gudanar a dakin taro na makarantar haddar Al’Qur’ani ta Sultan Maccido dake Sokoto.

Sai mun yaki cin hanci da rasahawa da kuma amfani da miyagun kwayoyi – Ibrahim Maishinku
Sai mun yaki cin hanci da rasahawa da kuma amfani da miyagun kwayoyi – Ibrahim Maishinku

"Mun zagaya jihohi tara a yekuwar da muke yi, kuma muna yunkurin zagaya sauran jihohin dake Najeriya domin aiwatar da yekuwar", inji Maishunku.

KU KARANTA KUMA: Tarihin rayuwa da siyasar 'Jagoran Talakawa' Aminu Kano

Kamar yadda muka sani cin hanci da rashawa na daga cikin babban kalubalen dake barazana ga arzikin kasar.

Zuwa yanzu gwamnatin shugaban kasa ta tara kudade da dama da ta kwato daga barayin gwamnati, sannan kuma ta sha alwashin kawo karshen rashawa a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng