Yan Shia sun jikkata Yansanda 22 a wata gumurzu da suka yi, sun lalata Motocin sintiri da dama

Yan Shia sun jikkata Yansanda 22 a wata gumurzu da suka yi, sun lalata Motocin sintiri da dama

Akalla jami’an Yansanda 22 ne suka jikkata a yayin wata arangama da suka yi da mabiya addinin Shi’a yayin da suke zanga zangar neman sako musu shugabansu, Ibrahim Zakzaky a babban binin tarayya Abuja, inji rahoton Daily Nigrian.

Rundunar Yansandan babban birnin tarayya ce ta sanar da haka a ranar Talata 17 ga watan Afrilu, inda tace a yanzu haka jami’an nata guda 22 na samun kulawa, sa’annan kuma sun lalata musu motocinsu na aiki da dama.

KU KARANTA: Tsaka mai wuya: Yadda aka hallaka wani matashi mai shekaru 20 a gidan wani fitaccen dan siyasa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan shi’an sun kai ma jama’a yan baruwana hari, sun tayar da hankulan jama’a tare da rufe hanya na tsawon lokaci, inda suka dinga fasa gilasan motocin mazauna unguwar Maitama, inda aka yi wannan bata kashi.

Yan Shia sun jikkata Yansanda 22 a wata gumurzu da suka yi, sun lalata Motocin sintiri da dama

Arangamar

Sai dai Kaakakin rundunar, Anguri Manzah ya tabbatar da kama tan shi’a guda 115, ya kara da cewa sun kwato gwafa, kwallayen boris, duwatsu, rodi, da sauran makamai, daga karshe yace zasu gurfanar da yan shi’ar a gaban kuliya manta sabo nan bada dadewa ba.

Bugu da kari Kaakaki Manzah ya gargadi yan shi’a da kada su kuskura su kara tare ma motoci hanya da sunan zanga zanga, don kuwa rundunar ba zata lamunci hakan ba, idan suka ji, zasu gamu da fushin hukumar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel