Wani Mutum ya kar abokin sa sakamakon kin amincewa da kwazabar sa ta neman Maza

Wani Mutum ya kar abokin sa sakamakon kin amincewa da kwazabar sa ta neman Maza

A ranar Talatar da ta gabata ne wata babbar kotu dake zamanta a garin Ikeja na jihar Legas, ta jefa wani Adebayo Ahmed gidan wakafi da laifin kashe abokin sa Samuel Owawu, sakamakon 'yar gardama da rashin amincewa da juna.

Alkalin kotun Bisi Akinlade, shine ya bayar da umarnin tsare Adebayo wanda ake zargin dan kungiyar asiri ne a gidan wakafi, kuma ya daga sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Mayu.

Misis Monisola Oshibogun, jami'ar 'yan sanda mai shigar da korafi ta shaidawa kotun cewa, tun a ranar 16 ga watan Janairu na shekarar 2016 da ta gabata ne Adebayo ya aikata wannan ta'addanci a unguwar Ifako Ijaiye ta jihar Legas.

Wani Mutum ya kaftawa abokin sa sara har lahira sakamakon kin amincewa da kwazabar sa ta Luwadi

Wani Mutum ya kaftawa abokin sa sara har lahira sakamakon kin amincewa da kwazabar sa ta Luwadi
Source: Twitter

Oshibogun ta bayyana cewa, rigima ta kaure ana tsaka da cacar baki kan wata wayar salula mallakin abokin mamacin da ya kasance dan neman maza.

Take cewa, "Marigayi Owawu tare da abokin sa Emeka Uche, sun karbi bakuncin wani abokin su Francis har gida."

"Francis wanda ya kasance dan neman maza nan da nan ya fara bayyana kwazabar sa ga Owawu inda shi kuma ya nuna bai san wannan zance ba."

"Wannan lamari ya sanya Owawu ya tara masa jama'a kuma aka fara tarawa Francis gajiya, inda a wannan lokaci Adebayo da wasu abokan huldar su suka nemi da a basu wayar salula mallakin Francis."

KARANTA KUMA: Jerin shugabanni 4 mafi karfin mulki a Duniya

"Owawu ya ki amincewa da bukatar su, inda ya dage da cewar akwai bidiyon Francis a yayin da yake aikata wannan bakin halin na sa kuma sai an gabatar shi ga hukuma domin ya kasance shaida."

"Nan na nan Adebayo da Owawu suka kaure da fada, wanda a yayin haka ne ya daɓa masa fasashiyar kwalba har cikin kirji."

Legit.ng da sanadin shafin jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, an garzaya da marigayi Owawu babban asibitin Ifako Ijaiye inda a nan ya ce ga garinku nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel