Idan ka ji Dattijon banza, Yaron banza ne: Yadda wani Dattijon biri ke biyan kananan yara N100 yana kwanciya dasu
Rundunar Yansandan jihar Legas ta gurfanar da wani mutumi Sikiru Gbadamosi gaban kuliya manta sabo, wata Kotun majistri dake zamanta a Ikorodu, kan tuhumarsa da laifin yi ma kananan yara fyade.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Sikiru ya kware wajen biyan kananan yara mata guda biyu, masu shekaru 11 da 13, Naira dari, N100 don yi musu fyade a gidansa mai lamba 8, titin Araromi, unguwar Ikorodu.
KU KARANTA Badakalar dala miliyan 462: Majalisar Dattawa ta bukaci Ministocin Buhari da gwamnan CBN su gurfana a gabanta
Dansanda mai shigar da kara, Sajan John Iberedem ya bayyana ma Kotu cewa SIkiru ya tafka wannan laifi ne a watan Maris da misalin karfe 2 na rana, inda ya tari yaran a lokacin da suke dawowa daga makaranta, ya basu naira N100 kowannensu a karo na farko, yayin da ya basu N1000 a karo na biyu.
Sai dai yaran sun bayyana cewa Sikiru ya dade yana kwanciya dasu, amma yana musu barazanar kisa muddin suka bayyana ma wani, inji rahoton majiyar Legit.ng.
Dansandan ya cigaba da cewa makwabta ne suka matsa ma yaran da tambaya, kan me suke zuwa yi a dakin mutumin nan, daga nan ne suka bayyana musu gaskiya, inda su kuma suka kai karar Dattijon birin ga Yansanda, daga bisani kuma aka garzaya da yaran zuwa Asibiti, inda aka tabbatar da yaga budurcinsu.
Bayan karanto masa laifukan da ake tuhumarsa dasu, Sikiru ya musanta dukkanin tuhume tuhumen gaba daya, laifukan da ka iya kai shi ga zaman gidan kurkuku na tsawon rayuwarsa.
Bayan kammala sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkalin Kotun F.A Azeez ta bada belin wanda ake tuhuma akan kudi naira miliyan daya, N1,000,000, tare da mutane biyu da zasu tsaya masa, su ma su biya naira miliyan daya, sa’annan a dage karar zuwa ranar 9 ga watan Mayu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng