Makiyaya sun fatattaki jama’a daga gidajen su a Jihar Nasarawa

Makiyaya sun fatattaki jama’a daga gidajen su a Jihar Nasarawa

- Wasu Makiyaya sun kai hari a wani Gari a cikin Jihar Nasarawa

- An far ma Mutanen Kabilar Tiv ne a sabon harin da aka kai jiya

- An kashe mutane akalla 32 an kuma kore jama'a daga gidan su

Labarin da ke zuwa mana yanzu shi ne akalla mutane 32 sun bar Duniya bayan da wani rikicin Makiyaya ya fada kan su. Wannan abu ya faru ne a wasu Kauyuka a cikin Jihar Nasarawa.

Makiyaya sun fatattaki jama’a daga gidajen su a Jihar Nasarawa

Jama'a sun ji ba dadi a hannun wasu Makiyaya

Wasu Makiyaya ‘Yan bindiga sun hallaka mutum sama da 30 na Kabilar Tibi a Garuruwan Awe, Keana, da kuma Doma. Jaridar The Nation tace an fatattaki sama da mutum 10, 000 daga gidajen su a dalilin wannan rikicin.

KU KARANTA: An gano masu hannu cikin rikicin Makiyaya da Manoma a Najeriya

Yanzu dai wadannan Bayin Allah ‘yan kabilar Tibi su na nan faman buya ne a hanyar Agwashi zuwa Jangwa bayan da aka tarwatsa muhallin su. Mun ji cewa wasu ma na kwance a asibiti a babban birnin Jihar watau Lafiya.

Kwamared Peter Ahemba wani Matashi a Yankin yace har yanzu Makiyayan da su ka fatattako jama’a daga gidajen su su na nan a a cikin Kauyen. Kwanakin baya ma an kai wani harin sai dai ‘yan Sanda sun ce duk ba su da labari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel