Dalillai 5 da kimiyya ta tabbatar na cewa cin naman Alade bashi da kyau bayan Musulunci da ya haramta

Dalillai 5 da kimiyya ta tabbatar na cewa cin naman Alade bashi da kyau bayan Musulunci da ya haramta

- Alade na daya daga cikin naman da akafi amfani dashi a fadin duniya, amma dai musulunci ya haramta cin namansa

- Bincike ya nuna cewa kai shekaru 70,000 ana cin naman Alade a tarihin duniya

- Naman Alade ana sanyashi cikin jan nama saboda kalarsa, kamar ja kamar kuma ruwan hoda, sakamakon haka yakeda hadari cin naman nasa

Alade na daya daga cikin naman da akafi amfani dashi a fadin duniya, amma dai musulunci ya haramta cin namansa. Bincike ya nuna cewa kai shekaru 70,000 ana cin naman Alade a tarihin duniya.

Naman Alade ana sanyashi cikin jan nama saboda kalarsa, kamar ja kamar kuma ruwan hoda, sakamakon haka yakeda hadari cin naman nasa bisa ga wadannan dalilai.

Dalillai 5 da kimiyya ta tabbatar na cewa cin nama Alade bashi kyau bayan Musulunci da ya haramta
Dalillai 5 da kimiyya ta tabbatar na cewa cin nama Alade bashi kyau bayan Musulunci da ya haramta

1. Naman Alade yanada kitse (Cholesterol) dayawa a cikinsa wanda idan ya shiga cikin mutum yana taruwa ne. Hakan yana sawa kitse na yin yawa a jinin mutum, wanda yake kawo shanyewar rabin jiki.

2. Cin nama Alade wanda ba’a dafa ba yana cinyo cututtuka da dama sakamakon kwayayen kwayoyin cuta da dama suna zama cikin nama Alade, wadanda idan suka shiga cikin mutum zasu cigaba da girma har su kai tsawon meter 4-10.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa nake takarar gwamna a Kano – Zaura

3. Cin sarrafaffen naman Alade kuma yana janyo ciwon Cancer, sakamakon sinadaran da ake amfani dasu wurin sarrafa naman wand ke hana kwayoyin cuta su daina yaduwa cikin naman.

4. Naman Alade yana da dauke da gubobi da dama da kuma kazanta, sakamakon yanda aka kiwatasu cikin gona yasa suke samun damar cin kashin abubuwa da dama wanda ta nan ne suke samun kwayoyin cuta a cikin namansu.

5. Naman Alade na kawo ciwon mura mai hadarin gaske, damar samu cutar murar daga cin naman Alade bata kai kiwon Aladen saurin kawo murar ba. Shiyasa wadan da ke bawa Alade abinci a gona inda ake kiwonsu yafi saurin kamuwa da cutar murar mai hatsari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng