Jirgin yakin hukumar soji MI-35M ya yi ruwan nakiyoyi a kan motocin 'yan Boko Haram

Jirgin yakin hukumar soji MI-35M ya yi ruwan nakiyoyi a kan motocin 'yan Boko Haram

Dakarun rundunar sojin sama masu aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno, Ofireshon Lafiya Dole, su ka yi ruwan wuta a kan motocin 'yan kungiyar Boko Haram a daren ranar 13 ga wata a AREGE mai nisan kilomita daga tafkin tekun Chadi.

Sanarwar da hukumar sojin sama ta fitar ta bakin darektan hulda da jama'a na hukumar, Olatokunbo Adesanya, ta ce tun farko wani jirgin yakin hukumar ne ya fara gano wasu motocin 'yan Boko Haram dauke da makamai na zirga-zirga a yankin ta hanyar amfani da na'urori na musamman dake cikin jirgin.

Jirgin yakin hukumar soji MI-35M ya yi ruwan nakiyoyi a kan motocin 'yan Boko Haram

Jirgin yakin hukumar soji MI-35M ya yi ruwan nakiyoyi a kan motocin 'yan Boko Haram

DUBA WANNAN: Za'a yiwa wani mutum bulala 80 saboda kirar surukarsa karuwa

Hukumar ta ce bayan samun wannan bayani ne sai ta aike da jirginta, MI-35M, mai saukar ungulu inda ya yi luguden wuta a kan motocin 'yan ta'addar.

A karshen ruwan wutar, hukumar sojin tayi nasarar lalata wata motar yaki ta 'yan ta'addar tare da dukkan mutanen dake ciki.

An kuma lalata karin wata motar tare da kashe wasu mayakan kungiyar yayin harin.

Hukumar sojin sama ta jaddada kudirinta na cigaba da bayar da gudunmawar ta ta hanyar cigaba da yin ruwan wuta a kan mayakan domin samar da kyakykyawan yanayin aiki ga dakarun soji na kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel