Ababe 8 da kwaskwarimar Masallacin Harami na Makkah ta kunsa

Ababe 8 da kwaskwarimar Masallacin Harami na Makkah ta kunsa

Rahotanni sun bayyana cewa tuni dai an fara gudanar da shirye-shirye na dashen laimomi a farfajiyar masallacin harami na birnin Makkah musamman a kusurwar sa ta Arewa, inda wasu kwararrun Injiniyoyi daga kasar Jamus ke kwangilar aikin.

Legit.ng ta fahimci cewa, Babbar cibiyar jagora kan harkokin Masallatai biyu Masu Tsarki, ita ce ke ruwa da tsaki wajen tabbatuwar wannan aiki na fadada masallacin tare da shinfida ta dashen laimomi da za su bayar da dama ta gudanar da ibadu cikin annashuwa a lokutan zafi.

Ababe 8 da kwaskwarimar Masallacin Harami na Makkah ta kunsa

Ababe 8 da kwaskwarimar Masallacin Harami na Makkah ta kunsa

Kamar yadda shugaban wannan cibiya kuma babban limamin masallacin harami na Makkah ya bayyana, Sheikh Abd al Rahman Al Sudais ya ce, wannan kwaskwarima tare da dashen laimomi ta zo ne da sanadin manufa ta tsohon Sarki Marigayi Abdullah Abd al Azeez da ya umarta tun a watan Dasumba na shekarar 2014.

KARANTA KUMA: 2019: Shehi Dahiru Usman Bauchi ya gargadi mabiyan sa kan yin Katin zabe

A yayin haka ne jaridar Legit.ng ta kawo muku wasu sirrika 12 da ba ku sani ba dake tattare da wannan aiki.

1. Za ayi dashen laimomi 8 a masallacin na harami masu girman gaske wanda ba bu makamantan su a duk fadin duniya.

2. An fara gudanar da dashen laimomin ne tun a farkon shekarar 2018.

3. Kowace laima za ta kunshi babban agogo domin duban lokaci.

4. Laimomin za su kunshi fuskoki domin su zamto jagororin tafarki ga masu bauta.

5. Za a sanya na'urori masu sanyaya daki domin daidaiton yanayi na zafi da kuma dalilai na tsaro inda za a dasa kyamarori masu daukar hoto da bidiyo.

6. Tsayin kowace laima zai kai kimanin mita 45 kuma nauyin ta zai kai tan 16. Hakazalika kowace laima za ta mamaye yankin na kimanin mita 2400 da zarar an buɗe ta.

7. Baya ga dashen wannan laimomi 8, za kuma a sake dashen wasu guda 54 cikin watanni 6 masu gabatowa.

8. Ana sa ran da zarar an kammala wannan aiki, masu bauta kimanin 400, 000 zasu amfana da inuwar laimomin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel