Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu

Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu

- Dole a nemo mafita kan tsattsamar dangantakar hukumomin tsaron sirri na kasar nan, inji Babagana Munguno

- Yanzu suna iya zuwa ganin shugaban kasa da kansu, shi yasa ake barin ofishin NSA a duhu

Mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro (NSA), Major General Babagana Monguno Mai ritaya, yace dole a cigaba da samun sa toka sa katsi tsakanin EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa (NIA) mutukar ba'a yi gyara ga dokar da ta kafa hukumomin tsaron ta shekara 1986 ba.

Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu

Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu
Source: Facebook

Mungunon dai ya bayyana damuwarsa kan yadda hukumomin tsaron suke cigaba da samun farraku a tsakaninsu maimakon su hada kai wajen yin aiki tare.

Amma ya alkanta hakan ne da rashin kwaskwarima da ba’a yiwa dokar da ta kafa hukumar dake kula da sha’anin tsaro ta kasa ba tun bayan kafuwarta.

Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu

Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu

Monguno ya fadi hakan ne a cikin rahoton kwamitin da majalisar dattijai ta kafa domin gano musabbabin rashin jituwar da aka samu tsakanin EFCC da DSS da kuma NIA a shekara da ta gaba.

Rikici tsakanin hukumomin ya faru ne a lokacin da jami’an EFCC suke kokarin kama tsohon shugaban hukumar liken asiri (NIA) ta kasa Mr Ayodele Oke da kuma tsohon shugaban hukumar DSS Mr Ita Ekpeyong.

KU KARANTA: An kama tsohuwa ‘yar shekara 75 zata shiga da kwayoyi kasar Saudiya

Babagana Monguno ya bayyana rashin jin dadinsa game da tabarbarewar dangantaka tsakanin hukumomin tsaron, a cewarsa, hakan na faruwa sakamakon hana ofishinsa kula da sauran hukumomin tsaron da dokar hukumonin tsaro ta 1986; ta Cap 278, Cap 278 LFN sashin 14 01-2 tayi, kasancewar suna da ikon ganin shugaban kasa a duk sanda suke so da kansu,

A don haka, lallai ya kama a samu sauyi a dokar, su dawo karkashin ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Munguno ya shaidawa kwamitin majalisar dattijan cewa, yana sane da irin tsamin dangantakar dake akwai tsakanin hukumomin tsaron, har ma ya kafa hujja da cewa shi bai da masaniyar EFCC tana yunkurin kama tsoffin shugabannin hukumomin tsaron sirrin kasar nan, har sai da ya karanta a jarida cewa, wasu jami’an tsaro sun hana su kama su.

Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu

Dalilin da yasa EFCC da DSS da kuma hukumar liken asiri ta kasa NIA suke fada a junansu

Yanzu haka dai sanatocin karkashin jagorancin Sanata Francis Alimikhena, sun cimma matsayar kara karfi ga ofishin mai bawa shugaban kasar domin ya zamto hukumomin tsaron sirrin na karkashinsa don kula da su a madadin shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel