Yadda Sani Sidi da abokansa suka kwashe biliyoyin kudi a NEMA - Aso Rock
- Fadar shugaban kasa ta bayyana yadda Sani Sidi da abokansa suka kwashe biliyoyin kudi a NEMA - Aso Rock
- Wani hadimin shugaban kasa ya ruwaito cewa tsohon shugaban NEMA Mohammed Sani Sidi ya rike sama da asusun banki 20 a bankuna mabambamta duk da aikin gwamnati yake yi
- Jami'in yace wai ma'aikatan da aka dakatar sun maza sun kai kara majalisar wakilai domin su tsayar da binciken hukumar yaki da almundahana ta kudade da burin a goyi bayan su
A jiya ne ofishin shuwagaban kasa ya sanar da yanda shuwagabannin NEMA suka wawure sama da biliyan daya, dala 284,000 da £95,000.
Wani jami'in shugaban kasa ya ruwaito cewa tsohon shugaban NEMA Mohammed Sani Sidi ya rike sama da asusun banki 20 a bankuna mabambamta duk da aikin gwamnati yake yi.
Jami'in yace wai ma'aikatan da aka dakatar sun maza sun kai kara majalisar wakilai domin su tsayar da binciken hukumar yaki da almundahana ta kudade da burin a goyi bayan su.
Yace"wannan kai tsaye yaci Karo da tabbatar da rashin laifin su da majalisar wakilai tayi karkashin kwamitin shirin gaggawa. Wadannan jami'ai suna da tambayoyi masu mahimmanci da zasu ansa; duk da dai wasu daga cikin jami'an sun fadi gaskiya, wasun su kuma sun kasa bayani akan kudi da kadarorin da aka gano nasu ne"
"Bisa ga rahoton da muka samu, Baza mu wanke su ba da goyon bayan da suke samu daga majalisar wakilai yana bayyana halin da Najeriya take ciki a inda manyan masu laifi suke boye kansu ta hanyar nuni ga wasu"
Kwamitin majalisar wakilan dai tayi kira da a maza a maida shuwagabannin kujerunsu, cewa da an dakatar dasu ba Bisa ka'idar shugabancin NEMA din karkashin kujerar Yemi Osinbajo.
Jami'in shugaban kasar yace akwai yuwuwar cewa akwai hadin baki tsakanin tsohon shugaban NEMA din da yan'kwamitin majalisar wakilan inda suka sace takardun NEMA don su wanke kansu.
DUBA WANNAN: Yadda aka kashe Zainab da diyarta a Legas
Wannan ya nuna cewa dakatar dasu aiki shi ne daidai saboda har yanzu ana bincike akan su gudun kada su sake sace shaidun da ake samu a al'amarin binciken.
Jami'in shugaban kasar yace nan ba da dadewa ba rahoton binciken zai kammala inda shuwagabannin NEMA zasu fuskanci hukunci.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng