Yadda Jama’a su ka tarbi tsohon Gwamnan Kano a Garin Shugaban kasa

Yadda Jama’a su ka tarbi tsohon Gwamnan Kano a Garin Shugaban kasa

- Sanata Kwankwaso ya kai ziyara har zuwa Garin Dauran Jihar Katsina jiya

- Tsohon Gwamnan ya je Daura ne domin ta’aziyyar Sanata Bukar Mustafa

- ‘Dan Majalisar yace Marigayi Galadiman na Daura abokin sa ne a Majalisa

A jiya ne tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata a yanzu Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai ziyara Garin Daura a Jihar Katsina domin ta’aziyya na rashin Sanatan Yankin da aka yi kwanakin bata.

Yadda Jama’a su ka tarbi tsohon Gwamnan Kano a Garin Shugaban kasa

Kwankwaso a fadar Mai martaba Sarkin Daura jiya da rana. Hoto daga: KwankwasoRM

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tafi Jihar Katsina ne a mota inda ya rika haduwa da dinbin masoyan sa a hanya. A lokacin da Sanatan ya kai Garin Malumfashi a Kudancin Jihar Katsina, masoya Kwankwasiyya sun fito masa lale.

KU KARANTA: Wani rikakken Farfesa ya fito takarar Sanatan Daura

Kamar yadda mu ka samu labari jama’a da dama sun fito da ja-ja-yen huluna a Daura inda nan ne Mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kwankwaso ya rubuta sunan sa cikin wadanda su ka zo ta’aziyyar Sanatan Yankin jiya.

Kwankwaso ya kuma dauki wannan damar inda ya gaida Mai martaba Sarkin Daura Umar Faruk Umar a fadar sa. Sanatan yace Marigayi Sanata Mustafa Bukar watau Galadiman Daura abokin sa ne kwarai da gaske a Majalisar Dattawan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel