An sake tono wata babbar badaqala ta N450m a tsakanin ministocin Jonathan

An sake tono wata babbar badaqala ta N450m a tsakanin ministocin Jonathan

- Almundahanar kudi: Yadda na biya tsohuwar minista da wasu mutane biyu Naira miliyan 450 inji wata shaida

- Mai shari'ar, Musa Kurya ya dage sauraron shari'ar zuwa 17 da 18 ga watan Mayu, 2018

- An dai tafka sata a lokacin mulkin Jonathan

An sake tono wata babbar badaqala ta N450m a tsakanin ministocin Jonathan

An sake tono wata babbar badaqala ta N450m a tsakanin ministocin Jonathan

Wata shaida Mrs. Annet Gyen shugabar aiyuka ta bankin Fidelity, reshen jos a 2015 ta sanar da babban kotun tarayya ta jos yanda ta biya tsohuwar ministan ruwa Mrs. Sarah Reng Ochekpe, tsohuwar shugabar jam'iyyar PDP a jihar filatu, Raymond Dabo da shugaban kamfen din Jonathan na jihar, Leo Sunday Jitong.

Za a iya tunawa a kara mai lamba FHC/J/141C/2017,hukumar yaki da almundahana ta kudade (EFCC) ta yi karar Ochekpe da sauran biyun a babbar kotun Gwamnatin tarayya dake jos a sakamakon almundahana ta Naira miliyan 450.

A zaman da akayi yau ne, Gyen wacce a yanzu itace manajan Bankin Fidelity reshen jami'ar jihar Benue kuma shaidar hukumar yaki da almundahana ta kudi ta sanar da kotun yanda wadanda ake zargi suka zo bankin a jos a shekarar 2015 domin fitarda Naira miliyan 450.

"na samu sako ta yanar gizo daga ofishinmu na Legas cewa Sarah Ochekpe, Raymond Dabo da Leo Jitong zasu zo reshen mu su fitar da Naira miliyan 450. Bamu da kudin a reshen mu, wannan dalilin yasa naje bankin Najeriya reshen jos bayan bin ka'idoji na karbo Naira miliyan 450 na kai bankin mu. Suka zo bankin mu kuwa suka karba."

Gyen ta kara da cewa "na tantance su ne ta hanyar duba katinsu na shaida bayan haka na basu kudin"

DUBA WANNAN: Yadda kannen Amarya ke dana ango don gwada kwarinsa a wata kabila

"Sarah ta nunamin shaidar ta ta ma'aikatar ruwa ta tarayya, shi kuma Raymond Dabo ya nuna katinshi na zabe, shi kuma Leo ya nuna min lasisin shi ba tuki ne. Sannan na basu takardun fitarda kudi inda aka bukaci da su rubuta sunayen su, sa hannun su da lambobin wayoyinsu" bayan sun cike sharuddan ta biya wadanda ake zargi kudin.

Mai kare wadanda ake zargi, Sunday Oyawole ya bukaci kotun ta yi watsi da wannan shaidar dalilin kuwa shi ne wacce ta ke shaidar ba ita ta kirkiri takardun da sukayi amfani dasu kafin fitarda kudin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel