Daga Chibok zuwa Lagos: Yadda wasu masu gudun hijira ke fama a 'cunkus dakin tsumma'

Daga Chibok zuwa Lagos: Yadda wasu masu gudun hijira ke fama a 'cunkus dakin tsumma'

- Mercy Solomon 'yar asalin garin Chibok dake jihar Borno. Garin da yayi suna sakamakon sace yam'mata 276 yan makaranta a ranar 14 Afrilu, 2014

Labarin ta na tattare da bakin ciki da rashi ballantana yaranta. Basu zuwa makaranta saboda bata da halin kaisu makarantar gwamnatin Legas duk da kyauta ne

Daga Chibok zuwa Lagos: Yadda wasu masu gudun hijira ke fama a 'cunkus dakin tsumma'
Daga Chibok zuwa Lagos: Yadda wasu masu gudun hijira ke fama a 'cunkus dakin tsumma'

A matsayin ta na yan'gudun hijira an tauye mata hakkokinta da dama kama rasa gurin zama na kusan shekaru 9. Ta kuma dogara ne da wasu domin samar da abubuwan rayuwa.

Daga Chibok zuwa Lagos: Yadda wasu masu gudun hijira ke fama a 'cunkus dakin tsumma'
Daga Chibok zuwa Lagos: Yadda wasu masu gudun hijira ke fama a 'cunkus dakin tsumma'

Daga cikin mummunan halin da suke ciki ya hada da rashin ingantacciyar kiwon lafiya. Akwai ire iren mercy da yawa a Legas.

Labarin ta na tattare da bakin ciki da rashi ballantana yaranta. Basu zuwa makaranta saboda bata da halin kaisu makarantar gwamnatin Legas duk da kyauta ne.

Daga Chibok zuwa Lagos: Yadda wasu masu gudun hijira ke fama a 'cunkus dakin tsumma'
Daga Chibok zuwa Lagos: Yadda wasu masu gudun hijira ke fama a 'cunkus dakin tsumma'

Mercy Solomon yar' asalin garin Chibok dake jihar Borno. Garin da yayi suna sakamakon sace yam'mata 276 yan makaranta a ranar 14 Afirilu, 2014.

"Da gaske makarantar gwamnati kyauta ce a Legas amma yarana zasu bukaci kayan makaranta, takalman makaranta, abincin da zasu je dashi makaranta, litattafai da kuma kudin mota. Wanda ni kuwa banda kudin" a cewar Mercy.

Mercy na daya daga cikin yan'garin Chibok wadanda suka bar garin sakamakon takurawar yan'ta'adda wanda yayi sanadiyyar watsa mutane sama da miliyan 1.8 yan'asalin jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Kamar yanda mercy ta fada, tana daya daga cikin yan'gudun hijira masu sa a domin kuwa wani mutum Dan kabilar Urhobo ya bata daki a gidan shi. Dakin ya kunshi kujerun roba amma babu katifa. A don haka ne mercy da yaranta suke barci akan tabarma.

"A da akwai wata mata da ke ara min kudi in biya musu kudin makaranta, ita sai in dinga biyanta kadan da kadan. Toh bana iya biyanta shiyasa ta daina bani. Nakanyi amfani da kudin ne ina saro tattasai, na kan kasa hada jarin ma shiyasa ta daina bani"

DUBA WANNAN: Tallafi don farfado da harkar manja

"Boko Haram sun kwace mana gari. Babu kowa a Chibok saboda sun fatattake mu, sun kona gidajen mu da gonakinmu, sun kuma kashe mana mutane. Nazo Legas a motar daukan kaya kuma nayi shekaru fiye da uku" inji wani mutum mai suna Martins.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng