Ga koshi ga kwanar yunwa: An hallaka wani matashi bayan ya ciyo naira miliyan 11 a caca

Ga koshi ga kwanar yunwa: An hallaka wani matashi bayan ya ciyo naira miliyan 11 a caca

Wani matashi mazaunin unguwar Sabo Pegi dake cikn garin Lafia na jihar Nassarwa ya gamu da ajalinsa a hannun wasu miyagun mutane bayan ya ciyo ribar naira miliyan goma sha daya, 11, a cacar ‘Naijabet’

An dai tsinci gawar wannan matashi ne mai suna Achuku Joseph da safiyar ranar Asabar 14 ga watan Afrilu a gefen hanyar zuwa jami’ar gwamnatin tarayya dake garin Lafiya, inda aka tsinci gawar tasa ta sha sara.

KU KARANTA: Baki shi ke yanka wuya: Wani matashi ya sha bulalar kazafi 80 sakamakon aibanta sirikarsa da sunan ‘Karuwa’

Jaridar The Nation ta ruwaito wani dangin matashin yana fadin cewa tun bayan da Achuku ya ciyo makudan kudaden ne wasu miyagun abokannansa suka fara bin sawunsa ba tare da ya ankara ba, bayan sun yi barazanar kashe shi muddin bai raba kudin dasu ba.

“Achuku ya yi ta tashi daga waje zuwa waje don buya daga miyagun mutanen dake nemansa, inda har ta kai ga suna fara amfani da tsafe tsafe wajen jifarsa, wanda hakan yayi sanadiyyar fara rashin lafiya, har ta kai ga ya samu matsala a kwakwalwarsa.

“Daga bisani mun gayyato wani Fasto da yayi masa addu’a, inda bayan nan muka garzaya da shi zuwa Asibitin kwararru na Dalhatu Araf dake garin Lafiya, domin ya samu Lafiya, a asibitin ne muka gano wasu tsubbace tsubbace a aljihunsa, inda muka cire su, daga nan sai ya fara farfadowa.” Inji shi.

A ranar da ya gamu da ajlinsa kuwa, majiyar Legit.ng ta ruwaito asubanci Achuku yayi ya fita daga gida zuwa inda babu wanda ya san inda ya shiga, sai da gari ya waye aka tsinci gawar ta sa a gefen hanya.

Sai dai sashin binciken manyan laifuka na rundunar Yansandan jihar ta fara gudanar da bincike kan kisan, tare da yin alwashin gano masu hannu cikin kisan na sa, a yanzu dai suna rike da gawar Achuku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng