2019: Fashola zai karbi mulki daga hannun shugaba Buhari – Babban limami

2019: Fashola zai karbi mulki daga hannun shugaba Buhari – Babban limami

- Prophet George Fakolade shugaban cocin Divine Intelligence Ministry ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Ofishinsa na shugaban kasa a shekarar 2019

- Prophet Fakolade yace a shekarar 2019 ‘yan Najeriya zasu zabi ministan wutar lantarki da ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yam aye gurbin shugaban kasa

- Fakolade yace kafin ya karbi Ofishin zai tsara wanda zaiyyi aiki dasu don magance rashawa a kasar, kuma ba zai dagawa kowa kafa ba, kuma zai gyara kasar ya magance duk wata matsala dake bibiyarta

Prophet George Fakolade shugaban cocin Divine Intelligence Ministry ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Ofishinsa na shugaban kasa a shekarar 2019.

Prophet Fakolade ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labare a karshen makon nan daya wuce, yace a shekarar 2019 ‘yan Najeriya zasu zabi ministan wutar lantarki da ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yam aye gurbin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Fakolade yace kafin ya karbi Ofishin zai tsara wanda zaiyyi aiki dasu don magance rashawa a kasar, kuma ba zai dagawa kowa kafa ba, kuma zai gyara kasar ya magance duk wata matsala dake bibiyar kasar.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya rasu jim kadan bayan ya sanar da rasuwar matarsa a Facebook

Yace Darakta Janar na Hukumar ‘Yan Sanda masu farin kaya (DSS) Lawal Daura, zai cigaba da rike Ofishinsa a karkashin Fashola don cigaba da ayyukan da mutanen kasa keso, kamar yanda yake gudanar dasu.

Ya kara da cewa Babatunde Fashola dan jihar Legas mutum ne wanda Allah ya zaba, ya zama shuagaban kasa a Najeriya a shekarar 2019

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng