Halima daya daga cikin direbobin manyan motan Dangote

Halima daya daga cikin direbobin manyan motan Dangote

- Halima Alhassan bazawarace mai yara uku wadanda nake kula dasu kuma kullun ina kokarin ganin na kyautata masu rayuwarsu

- Halima ta bayyana cewa ta bude makarantar koyon tukin babbar mota, don kara yawan mata cikin direbobin manyan motoci

- Hajia Rabiat Abubakar, wadda itace direbar babbar mota ta farko a Najeriya, itace tasa ta kara samun karfin gwiwa akan tukin babbar mota

Halima Alhassan bazawarace ‘yar shekara 41, ‘yar karamar hukumar Shendam a jihar Filato, mai yara uku wadanda nake kula dasu kuma nake kokarin kyautata masu rayuwarsu, yanzu haka danta na farko yana karatun likitanci a jami’ar Jos sauran biyun kuma suna makarantar sakandare.

Halima daya daga cikin direbobin manyan motan Dangote

Halima daya daga cikin direbobin manyan motan Dangote

A cewar Halima: "Na bude makarantar koyon tukin babbar mota, don kara yawan mata cikin direbobin manyan motoci a kasar nan wadda sana’ace da maza suka mamayeta.

"Hajia Rabiat Abubakar, wadda itace direbar babbar mota ta farko a Najeriya, itace tasa na kara samun karfin gwiwa akan tukin babbar mota, itace ta daukeni ta kaini wurin shuagaban direbobi Alhaji Uba Zariya, inda ya hadani da Alhaji Ishaku Paskere, wanda shine ya koya mani toki babbar mota.

KU KARANTA KUMA: Barayi kadai ke zama shuwagabannin kasa a Najeriya- Balarabe Musa

"Duk da dai mazan da muke harkar tare dasu suna nuna mana kishinsu sabode suna ganin cewa sana’ar mazace bata mata ba, amma dai hakanan nake hakuri tinda yanayin aiki ne ya kawo haka, amma dai ina kokarin inga na bude makarantar koyon tuki ta mata wanda hakan nake ganin zai magance matsalar tsagwama a aikin."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel