Barayi kadai ke zama shuwagabannin kasa a Najeriya- Balarabe Musa

Barayi kadai ke zama shuwagabannin kasa a Najeriya- Balarabe Musa

- Tsohon gwamnan jihar Kaduna Balarabe Musa yace ba wanda zai iya zama shugaban kasa a Najeriya idan ba tsohon barawo bane ko kuma barayi ne suka goya masa baya ba.

- Yace ai abun mamaki ne ta yanda za’ace mutum ya hada kudin kamfen din shugaban kasa a kasar nan tamu ta Najeriya

- Ya yi zargin cewa tattalin arzikin al’umma da ake kwashewa ana amfani dasu wurin tafiyar da lamuran siyasa, inda yace 99% na mutanen dake rike da matsayin barayi ne

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Balarabe Musa yace ba wanda zai iya zama shugaban kasa a Najeriya idan ba tsohon barawo bane ko kuma barayi ne suka goya masa baya.

Yace ai abun mamaki ne ta yanda za’ace mutum ya hada kudin kamfen din shugaban kasa a kasar nan tamu ta Najeriya.

Musa ya zargi tattalin arzikin al’umma da ake kwashewa, ana amfani dashi wurin tafiyar da lamuran siyasa, inda yace 99% na mutanen dake rike da matsayin, barayi ne, ya bayyana haka a wani bidiyo da aka sanya a kafar sadarwa ta Facebook.

Barayi kadai ke zama shuwagabannin kasa a Najeriya- Balarabe Musa
Barayi kadai ke zama shuwagabannin kasa a Najeriya- Balarabe Musa

Omoyele Sowore, shugaban kungiyar yada labarai a kafar sadarwa ta yanar gizo ta Sahara Reporters, a bidiyon yace ya ziyarci dan siyasar na jihar Kaduna, don sanin yanda ya tsara tafiyar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019.

KU KARANTA KUMA: 2019: Atiku ya kai ziyara kasar Ingila don ya karo suna

Bayan tambayar da akayiwa Balarabe dan shekaru 81, game da yanda tsofaffi suka rikita Najeriya yace hakan ya faru ne sakamakon hurdodin siyasa, yace idan baka mance ba “Shehu Shagari ya zama shugaban kasa ba tare da ya zama barawo ba”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng