Filla filla: Yadda Sanatoci ke bindiga da kudaden garabasa da suke samu a majalisar dattawa

Filla filla: Yadda Sanatoci ke bindiga da kudaden garabasa da suke samu a majalisar dattawa

Tun bayan da wakilin al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya bayyana makudan kudaden da ake antaya ma Sanatocin Najeriya, da yace sun kai naira miliyan 13 ne dai aka fara binciken kwakwaf game a kudaden da Sanatocin suke samu.

Premium Times ta ruwaito wani sabbin bayanai sun bankado wasu makudan kudade na daban da yan majalisar ke cabawa da su, baya da albashinsu, da kuma kudin ayyukan mazabu da suke sharba,

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige wani Dansanda a jihar Benuwe, Yansanda 11 sun yi ɓatar dabo

Bayanan da majiyar Legit.ng ta samar sun nuna cewa a kowanne wata, dukkanin majalisun dattawa, su 109 suna samun alawus alawus da suka hada da:

1- Naira miliyan daya da dubu dari takwas (N1.8m) kudin siyan jaridu kowanne watanni uku

2- Naira miliyan goma (N10m) na zirga zirga da yawace yawace a cikin Najeriya kowanne watanni uku

Filla filla: Yadda Sanatoci ke bindiga da kudaden garabasa da suke samu a majalisar dattawa
Sanatoci a majalisar dattawa

3- Naira miliyan daya da dubu dari biyar (N1.5) kudin duba lafiyar na’urar Kwamfuta kowanne watanni 3

4- Naira dubu ashirin (20,000) na siyan jarida a duk rana

5- daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2015 ana baiwa kowanne Sanata naira miliyan arba’in da biyar (N45m) a bayan duk watanni uku.

Ko a wannan zangon mulki daga shekarar 2015 zuwa 2018, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kashe ma Sanatoci naira biliyan 53 a matsayin kudaden hidimar yau da kullum.

Sai dai majiyar ta kara da cewa dokar majalisa ta bukaci kowanne Sanata ya kawo mata rasidin abubuwan da ya kashe kudaden da ya samu a majalisa, sai dai binciken majiyar ta ruwaito da dama daga cikinsu rasidin bogi suke bayawar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng